DSS ta ceto sakataren ƙaramar hukumar da aka sace a Kano
[ad_1]
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), ta ceto Sakataren Ƙaramar Hukumar Kibiya a Jihar Kano, Alhaji Hamza Durya, wanda aka sace, tare da kama mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin.
An sace Durya ne, a daren ranar Juma’a a gidansa da ke ƙauyen Durya a Karamar Hukumar Kibiya, bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari gidansa.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana wannan aiki a matsayin babbar nasara a yaƙi da aikata laifuka.
Ya ce jami’an DSS sun yi aiki cikin gaggawa da ƙwarewa, inda suka tabbatar an ceto Durya cikin ƙoshin lafiya.
Ya kuma ce an kama mutum biyu da ake zargi, duk da cewa sun samu raunukan harbin bindiga yayin artabun.
“Ƙananan hukumomin Jihar Kano na kallon wannan a matsayin abin farin ciki da kuma shaida jajircewa da ƙwarewar jami’an tsaronmu,” in ji Kwamishinan.
“Gwamna Abba Kabir Yusuf ya daɗe yana bayar da kayan aiki da goyon baya domin tallafa wa jami’an tsaro, kuma wannan nasara na nuna yadda dabarun da ake amfani da su ke aiki wajen yaƙi da laifuka a dukkanin ƙananan hukumomi 44 na jihar.”
Gwamnatin ta kuma buƙaci mazauna jihar su kasance masu sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba.
Ya jaddada cewar haɗin kan al’umma yana da muhimmanci wajen inganta tsaro.
Da yake magana bayan an ceto shi, Durya ya bayyana irin halin da ya shiga bayan sace shi.
Ya ce maharan sun shiga gidansa ne bayan sun tashi ɗansa daga barci tare da tilasta masa ya nuna musu inda yake.
Daga nan ne suka ɗaure shi da sarƙa, suka rufe masa ido, sannan suka kai shi wani wajen kiwon dabbobi da ke kusa a Ƙaramar Hukumar Rano.
“Sun ɗaure ni da sarƙa tare da rufe min fuska, sun tsare ni a ɗakin kaji da dabbobi,” in ji Durya.
“Dukkanin maharan suna magana da Fulatanci ne, kuma tsawon lokacin da nake tsare ban taɓa ganin sun yi sallah ba.
“Da farko sun buƙaci Naira miliyan 300, daga baya suka rage zuwa miliyan 100, sannan suka sake dage kan miliyan 100 bayan sun ce an faɗa musu ina da kusanci da Gwamnan Kano.”
Durya, ya kuma zargi cewa wani daga cikin al’ummarsa ne, ya yaudari masu garkuwar ta hanyar faɗa musu cewa yana da kuɗi masu yawa.
Ya ƙara da cewa ’yan bindigae sun fito ne daga Jihar Kaduna.
“Wani daga cikin al’ummata ne ya faɗa musu. Sun zo ne daga Rijana a Kaduna,” in ji shi.
Ya gode wa DSS bisa ceton rayuwarsa ba tare da an biya kud5in fansa ba.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, wanda ya bayyana sunansa da Nasiru, ya amince cewa sun fito ne daga Rijana a Jihar Kaduna domin sace sakataren.
Ya ce sun samu taimakon wasu makusantan sakataren.
“Mun zo daga Rijana, sannan daga baya aka kawo mana bindigogi. Mun kai kusan mutum 10, amma sauran sun tsere.
’Mu biyu ne aka kama, yayin da sauran suka gudu duk da sun samu raunukan harbin bindiga,” in ji Nasiru.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link