Kakakin Majalisar Zamfara da mambobi 12 sun koma APC

[ad_1]



Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Bilyaminu Moriki da wasu mambobin majalisar guda 12 sun sauya sheƙa daga daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Moriki ya sanar da sauyin sheƙar ne a yayin zaman majalisar da aka gudanar a Gusau ranar Litinin, bayan gabatar da takardun murabus dinsu a gaban majalisar.

Rahotanni sun nuna cewa matakin na zuwa bayan komawa jam’iyyar APC da gwamnan jihar, Dauda Lawal, ya yi bayan ficewa daga PDP.

Ana sa ran jam’iyyar APC za ta karɓi gwamnan a hukumance a wannan Talatar a wani ƙwarƙwaryan biki da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da shugabannin jam’iyyar na ƙasa, da kuma tsoffin gwamnonin jihar za su halarta.

Daga cikin ‘yan majalisar da suka sauya sheƙa har da mataimakin kakakin majalisa, Adamu Aliyu, shugaban masu rinjaye, Bello Mazawaje, da kuma Babban mai Tsawatar na majalisar, Rilwanu Nagambo, da sauransu.

Moriki ya ce sun ɗauki wannan mataki ne domin mara wa gwamna Lawal baya wajen samar da ci gaba a jihar, tare da inganta haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jiha da ta tarayya.

Da wannan sauyin, jam’iyyar APC ta samu cikakken rinjaye a Majalisar Dokokin Zamfara, inda yanzu take da dukkan kujeru 24 na majalisar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *