Matatar Dangote Ta Fitar Da Tan 456,000 Na Man Fetur Zuwan Wasu Ƙasashen Afrika

[ad_1]

Matatar mai ta Dangote ta fara aike tataccen man fetur zuwa wasu ƙasashen Afrika.

Wannan ya biyo bayan iƙirarin da ta riga ta yi ma cewar ta wadatar da kasuwar cikin gida a Nijeriya, duk da cewa har yanzu farashin mai yana da tsada a gidajen mai.

  • An Kashe Ƴan Ta’adda 500 A Hare-haren Ngoshe Da Fatori – Zulum
  • Daƙile Taron Ƙasa Na Abuja: Ɓangaren PDP Ƙarƙashin Turaki Ya Caccaki Ɓangaren Wike

Rahotanni sun nuna cewa an tura manyan jiragen ruwa guda 12, ɗauke da kusan tan dubu 456 na man fetur, zuwa ƙasashe biyar na Afrika.

Waɗannan ƙasashe suna fama da matsalolin makamashi sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya.

Kafafen yaɗa labarai sun ce an riga an sayar da wannan man fetur, wanda ke nuna cewa ƙasashen suna matuƙar buƙatarsa.

Ƙasashen da suka karɓi man fetur ɗin sun haɗa da Côte d’Ivoire, Kamaru, Tanzania, Ghana da Togo.

Hakan na nuna yadda matatar Ɗangote ke ƙara bunƙasa tun bayan da aka kafa ta.

Wani jami’i a matatar, wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya ce wannan nasara na nuna ƙarfin Nijeriya a fannin makamashi da kuma kasuwanci.

Adadin tan dubu 456 na man fetur ya kai kusan lita miliyan 608.

Wannan zai taimaka wajen ƙarfafa masana’antar mai da kuma ƙara yawan ciniki a kowace rana.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *