Tinubu Ya Yi Wa Dimokuraɗiyyar Nijeriya Shaƙar Mutuwa – Atiku
[ad_1]
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan Nijeriya kuma jigo a jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, cewa Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi wa dimokuraɗiyyar Nijeriya shaƙar mutuwa.
Ya babbana haka ne a lokaci da yake yin gargaɗi kan ƙarancin yawan masu jefa ƙuri’a da aka samu a zaɓen shugaban ƙananan hukumomi na Babban Barnin Tarayya, Abuja da aka gudanar a ranar Asabar.
- Atiku Ya Nemi Gwamnati Ta Fayyace Dalilin Tsare El-Rufai
- Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku A Saudiyya
Atiku ya bayyana siffata lamarin na cewa kashi kashi 20 cikin dari na masu jefa ƙuri’a suka fito yin zaɓe a Abuja, wanda ya nuna halin tsanani da dimokuradiyyar Nijeriya ƙarƙashin gwamnatin Tinubu ta shiga ciki.
A cewarsa, irin wannan karancin halartar jama’a a babban birnin ƙasar haɗari ne mai girma, an dai samu haka ne sakamakon girɓata siyasa ta hanyar rashin kishi da tsoratarwa, da rage ƙarfin muradun masu adawa.
Sai dai kuma Atikun ya zargi gwamantin Tinubu da rage Ƴancin dimokuraɗiyya da tsangwama ga masu adawa, da haɓaka yanayi na tsoratarwa, inda ake ɗaukar ra’ayoyin siyasa na daban a matsayin barazana.
“A duk lokacin da ƴan ƙasa suka rasa aminci a ɓangaren zaɓensu, to dimokuraɗiyya na gab da fara mutuwa. Wannan lamari ba kawai rashin sha’awar yin zaɓe bane. Ana murƙushe dimokuraɗiyya ne kawai a Nijeriya, wannada a hankali ana shiga cikin haɗari,” in ji shi.
Atiku ya yi gargaɗin cewa ci gaba da lalacewar sha’anin shugaban na iya jawo babbar illa ga dimokuraɗiyya na ƙasa. Sannan kuma ya yi kira ga jam’iyyun adawa da su haɗa kai wajen samun nasarar kifar da wannanan gwamnati.
“Wannan lamari ba batun gazawar jam’iyyun siyasa ba ne, batun kare jamhuriya ne. Lokaci ya yi da za mu tsaya tare domin cetowa da sake gina Nijeriya a wannan lokaci,” in ji shi.
[ad_2]
Source link