Binciken CGTN: Shagalin Bikin Bazara Na Sinawa Ya Zama Hanyar Nuna Sabon Karfin Samar Da Hajoji Da Hidimomi Masu Karko Na Kasar Sin

[ad_1]

Amfani da fasahar tsalle da jujjuyawa, da sabon salon raye-raye, da ingantacciyar mu’amalar bil’adama da mutum-mutumin inji, gwaninta da abubuwa masu jan hankali da mutum-mutumin injin masu siffar dan’adam suka nuna a shaglin bikin bazara da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ya gudanar, wanda ya kasance shirin talabijin da ake ribibin kallo a duniya domin bikin sabuwar shekarar gargajiyar Sinawa, na ci gaba da samun bunkasa.

Wani binciken jin ra’ayoyi na duniya da CGTN ta kaddamar ya nuna cewa, kashi 94% na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun dauki shagalin bikin bazara na CMG a matsayin wani muhimmin dandali da ke baje kolin sabbin fasahohin kimiyya da fasaha na kasar Sin, inda mutum-mutumin injin masu siffar dan’adam ke fayyace ci gaba mai zurfi da ake samu a bangaren raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko na kasar Sin.

“E, kasar Sin ce!” Wani mai amfani da shafin intanet dan kasar Aljeriya ya ambaci mutum-mutumin injin masu siffar dan’adam da “abin mamaki”. “Da farko, na kasa yarda da cewa su mutum-mutumin inji ne—saurinsu, yadda suke yin abu cikin kwarewa musamman kuma tsarinsu na aiki da juna ya kasance abin al’ajabi. Abu mafi burgewa kuma a ciki duka, babu kuskure ko daya!”

Samuwar mutum-mutumin inji masu siffar dan’adam a dandalin shagalin bikin bazara cikin hanzari, ya nuna wa masu kallo na duniya saurin ci gaban masana’antun kere-keren mutum-mutumin inji da kayayyaki masu aiki da fasaha na kasar Sin, wanda hakan ya kara karfafa kwarin gwiwa kan makomar kirkire-kirkiren fasaha ta kasar Sin. Tun daga kan manhajar DeepSeek zuwa jirage marasa matuki da kuma mu’amala ta fasaha, kashi 88.2% na masu bayyana ra’ayoyi sun yi imanin cewa kasar Sin tana kan gaba a duniya ta fuskar aikace-aikacen fasahar kirkirarriyar basira.

An gudanar da kuri’ar jin ra’ayoyin ce a sassan dandalolin CGTN na Turanci, Sifaniyanci, Faransanci, Larabci, da Rashanci, wanda ya jawo hankulan mutane 13,514 wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 40. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *