Sojoji sun kama ɓarayin shanu da ƙwato makamai a Filato

[ad_1]



Dakarun runduna ta 3 da rundunar haɗin gwiwa – Operation Enduring Peace (JTF OPEP) masu wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato sun kama wasu da ake zargin ɓarayin shanu ne a ƙauyen Kogul da ke Ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato.

A cewar rundunar, kama waɗanda ake zargin ya biyo bayan ƙoƙarin da sojojin suka yi ne don daƙile barazanar satar shanu, “wanda ke haifar da rikici a yankin da Rundunar haɗin gwiwa ta ke.”

Da yake yi a wa manema labarai bayan ikan nasarar da rundunar ta samu a Jos, a ranar Alhamis, kakakin rundunar, Manjo Samson Zhakom, ya ce a wani samame na sirri da aka gudanar a ranar 11 ga watan Satumban 2025 a maɓoyar waɗanda ake zargin.

Sojojin sun kuma ƙwato makamai da alburusai da suka haɗa da bindiga ƙirar AK-47 ɗaya, ƙunshin alburusai na bindigar AK-47 guda ɗaya, bindiga ƙirar reɓolɓer, da alburusai ƙirar 7.62 da wayoyin salula da kuɗi.

Manjo Zhakom ya ce waɗanda ake zargin da kuma kayayyakin da aka ƙwato suna hannun sojoji domin ci gaba da bincike.

Ya ƙara da cewa sojoji suna gudanar da aikin bibiya domin kame wasu rukunin masu aikata laifuka, yana mai jaddada cewa, “wannan kamun yana da matuƙar muhimmanci ga ƙoƙarin da ake yi na shawo kan matsalar rikicin, wanda dakarun runduna ta 3/JTF OPEP ke ƙoƙari sosai kuma suka lashi takobin daƙile matsalar a yankin tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *