Kasuwancin zobe ya kai ni ƙasashen waje

[ad_1]



Wani mai kasuwancin sayar da azurfa, Malam Idris Adamu Azare ya ce,  a dalilin sayar da azurfa da yake yi fiye da shekara 26 sai da ya zaga jihohin ƙasar nan 31 da kuma wasu ƙasahe 2 na Afirka ta Yamma.

Malam Idris ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Aminiya a kan yadda yake gudanar da harkokinsa na kasuwancin sayar da azurfa.

Ya bayyana cewa, wannan kasuwanci na zurfa kasuwanci ne da ya fara shi tun shekarar 1999, kuma tun daga wancan lokaci babu abin da yake tattare da wannan kasuwancin sai riba da kuma alheri, inda akan samu faɗuwa, domin babu wani kasuwanci da mutum zai ce shi a kullum yana cikin samun riba, amma dai harkar ita azurfa, musamman in aka ce ka ci karo da wanda ya san muhimmancinta to duk farashin da ka faɗa masa haka zai ɗauka ya ba ka.

Sai dai kuma in ka haɗu da mutumin da bai san muhimmancinta ba to duk darajar kuɗinta sai ka ga ya taya maka kuɗin da bai taka mara ya karya ba, ma’ana ƙasa sosai da yadda kaima ka saye ta.

Haka nan in kuma ka kai talla wurin mutanen da suka san darajar azurfa to ai a ranar za ka tarar da an maka cinikin da ba ka yi tsammani ba.

A cewar Malam Idris, matuƙar mutum zai sa gaskiya a lamarinsa to a gaskiya zai ga fa’ida matuƙa, domin in mutum yana sayar da azurfa ta ƙwarai da babu coge a tattare da ita to in Allah Ya so za ka samu dacewa a harkokin kasuwancinka, amma matuƙar ka tsayar da rashin gaskiya a kasuwancin na azurfa to lallai za ka ga ba daidai ba.

A nan sai Aminiya ta tambaye shi ko yaya batun coge yake a kasuwancin azurfa? Sai ya amsa da cewar, ‘‘abin da yake nufi da coge shi ne mutum.ya ɗauki wani zobe na gorar ruwa (tagulla) ko kuma wani zobe da aka yi shi da ƙarfe ya ce ai azurfa ce, ya kuma sayar wa mai saya. Ai ka ga ya yi masa coge, ya sayar masa abin da ba azurfa ba da sunan azurfa.”

Da ake tambayar sa a kan to yaya suke gane zobe na azurfa da wanda ba na azurfa ba?

A nan ma sai ya amsa da cewar, “ai duk wanda yake kasuwanci irin na azurfa ko zinare ba za ka rasa samun wani sinadarin da muke amfani da shi ba don tabbatar da zoben azurfa mai kyau ko wanda ba na azurfa ba. Wannan shi ne gaskiyar magana.”

Malam Idris ya kuma bayyana irin fa’idar da ya samu a wannan kasuwanci nasa na sayar da azurfa, inda ya ce, da farko ya samu ilimi na sanin rayuwar duniya sanadiyyar wannan kasuwanci nasa, domin ya shiga aƙalla ƙasashen biyu na Afirka da suka haɗa da Jumhuriyar Nijar da kuma ƙasar Kamaru kana ya zaga jihohin ƙasar nan aƙalla 31, waɗanda dukkansu ya shiga manyan biranensu wajen gudanar da kasuwancin sayar da azurfa, kuma waɗannan tafiye tafiye sun sa ya samu ilimin zaman duniya da ba ya misaltuwa.

Baya ga ilimin zaman duniya da ya samu, har ila yau ya samu damar mallakar gidaje aƙalla biyu da filaye abin sai godiya,  domin cikin wannan kasuwanci nasa har ya auri mata kuma Allah Ya arzurta shi da ‘ya’ya maza da  mata.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *