Dorinar ruwa ta talauta al’ummar Daɗin-kowa

[ad_1]



Al’ummar garin Daɗin-kowa da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba a Jihar Gombe na fuskantar wata babbar barazana ta rayuwa da tattalin arziki, sakamakon yawaitar dorinar ruwa a Madatsarruwa ta Daɗin-kowa, lamarin da ya durƙusar da manyan sana’o’insu na noma da kamun kifi, tare da haddasa asarar rayuka da dukiya.

Binciken da wakilinmu ya gudanar ya nuna cewa, ɓarnar dorinar ta kai wani mataki da ke barazana ga ci-gaba da tsaro da walwalar al’umma a yankin, inda dubban iyalai ke rayuwa cikin fargaba da matsanancin talauci, wanda magidanta da masu kamun kifi suka bayyana baƙin cikinsu kan halin da suke ciki ga kuma babu kulawar gwamnati.

Rushewar sana’o’in gargajiya

Sarkin Ruwa na garin Daɗin-kowa, Malam Abubakar Sa’adu ya bayyana cewa, abin da ke faruwa ya wuce barazana ta muhalli, yana rikiɗewa zuwa matsalar jin-ƙai da tattalin arziki.

Sarkin Ruwa ya ce, manoma da ke iya girbin buhunhuna da dama a shekarun baya sun daina noma gaba ɗaya, yayin da masunta fiye da dubu ɗaya da ke rayuwa a garin na Daɗin-kowa suke sana’ar kamun kifi, sun haƙura da shiga ruwa saboda tsoron rasa rayukansu.

“Yanzu noma ya tsaya, kamun kifi ya tsaya. Mutane suna zaune ba aikin yi, ba abin dogaro da kai,” in ji Sarkin Ruwa.

Asarar rayuka da fargabar kullum

Rahotanni daga al’umma sun nuna cewa, an rasa rayukan mutane da dama a shekarun baya-bayan nan, yayin da wasu kuma suka tsira da munanan raunuka.

Wannan ya sa mazauna yankin ke ƙaurace wa kogin duk da cewa shi ne ginshikin rayuwarsu.

Suleiman Abubakar, ɗan uwan Sama’ila Abubaakar, wani da dorinar ta fasa masa ƙirji, ya ji munanan raunuka sakamakon harin dorinar a bakin kogi, ya bayyana cikin takaici cewa, abin da ke faruwa yana nuna gazawar kare rayuwar al’umma daga hukumomi.

“Ba abin yarda ba ne a ce, dabba na halaka mutane, ana kallon mu. Rayuwar ɗan-adam ta fi komai daraja,” in ji Suleiman.

Ya ce, ba kawai batun jikkata ba ne, har da lalata gonaki da ruguza hanyar samun abin rayuwa, lamarin da ya jefa iyalai da dama cikin yunwa.

Ya ce, ƙaninsa Sama’ila ya je bakin kogi sayen kifi ne sa’adda dorinar ta cafke shi, ta fasa masa ƙirji ta karya shi a ƙafa, inda jama’a suke ceto shi da kyar yanzu yana gadon asibiti, yana jinya an sanya masa iskar oksijin.

Suleiman ya ƙara da cewa, gwamnati ta kawo musu ɗauki fa kafin abun ya ta’azzara, domin haƙurinsu ya fara ƙarewa, saboda ba za su zuba ido suna ganin dabba na kashe su, su haƙura ba.

Wani masani kan harkokin al’umma, mai suna Aƙilu Gyara Sa’a Garin Abdullahi ya bayyana cewa, abin da ke faruwa a Daɗin-kowa ya wuce matsalar muhalli, yana rikiɗewa zuwa barazanar tsaro da jin-ƙai.

A cewarsa, idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, yankin na iya fuskantar ƙaura da rashin aikin yi da ƙaruwar matsalolin zamantakewa.

“Duk lokacin da ka hana mutane noma da kamun kifi, ka hana rayuwa ce gaba ɗaya,” in ji Aƙilu.

Dalilin yawaitar dorinar ruwa

Masu ruwa da tsaki sun danganta yawaitar dorinar da canjin yanayin ruwa tun bayan fara aikin samar da wutar lantarki, wanda ya sa ruwan kogin ke tsayawa tsawon lokaci, yana ba wa dorinar damar hayayyafa ba tare da tangarda ba.

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar yankin, Inuwa Garba ya bayyana cewa, matsalar ta kai matakin da ke buƙatar haɗin gwiwar gwamnati da hukumomin da abin ya shafa.

A cikin jawabin da ya gabatar a zauren majalisa kan batun ɗaukar matakin tarayya, domin ganin an samar da mafita mai ɗorewa.

“Ba za mu bari al’ummarmu su ci gaba da rasa rayuka da dukiya ba. Wannan batu ne da ya shafi tsaro da muhalli da rayuwar jama’a,” in ji Inuwa Garba.

Ya ce, akwai buƙatar ɗaukar matakai kamar kula da namun daji da rage yawaitar dorinar da kare rayukan manoma da masunta.

Al’ummar Daɗin-kowa, na kira ga Gwamnatin Tarayya da ta jihohi da su ɗauki mataki cikin gaggawa, domin kare rayuka da farfaɗo da tattalin arzikin yankin.

Wani da dorinar ta taɓa karyawa

Abdulmumini Baƙo da ake kira Abdullahi Gunji, wanda dorina ta karya shi a wani hari da ta kai masa a lokacin da yake kamun kifi shi da ƙaninsa ya ce, suna cikin jirgin ruwa kawai ba su ankara ba sai dorina ta ɓullo ta ƙasan jirginsu, ta kifar da su, ta kama cinyarsa ta karya shi kuma ƙanin ya tsira da kyar, wanda da taimakonsa ne da jama’a aka taru, aka ceto shi.

Ya ce, har ya yi jinya ya warke babu tallafin gwamnati da ya samu, inda ya ce hakan ba a kyauta masa ba.

Abdullahi Gunji ya koka matuƙa inda ya ce, ban da asarar amfani gona, sun rasa rayukan mutane a sanadiyyar ɓarnar dorinar ruwan.

Al’ummar yankin sun ce, kiransu ga gwamnati shi ne, ko a kashe dorinar ko a san yadda za a yi a ɗebe su daga ruwan, domin sun zama bala’i.

Saboda manoma da masunta duka ba wanda ya tsira, domin yanzu haka a gonakansu ba wanda ya yi noma saboda tsoron dorina.

Aminiya ta yi ƙoƙarin ganin ta zanta da Sama’ila da dorinar ta fasa wa ƙirgi har kayan cikinsa suka fito, wanda a halin yanzu yake kwance a asibiti, amma ya ci-tura domin yana sanye da naurar samar da numfashi ta oɗygen.

’Yan Sanda

A ɓangaren ’yan sanda, wakilinmu ya kira Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi don jin ko sun samu labarin ta’adin dorinar ta kuma yadda take kashe jama’a, sai ya ce, bai da labara, amma zai bincika, ya ji ko an turo musu, sannan zai kira, amma har zuwa lokacin aiko da labarin nan bai kira ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *