Majalisa ta amince da ɗaurin shekara 2 ga duk wanda aka samu cikin jam’iyya sama da ɗaya
[ad_1]
Majalisar Wakilai ta yi gyara sashe na 77 na sabuwar Dokar Zaɓe ta 2026, inda ta tanadi hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari ko biyan tarar Naira miliyan 10 ga duk wanda aka samu cikin jam’iyyun siyasa biyu a lokaci guda.
Aminiya ta ruwaito cewa ’yan majalisar sun yi wannan gyara ne bayan muhawara mai zafi, inda suka ƙara yin gyara a sashe na 8, 9 da kuma 10 a cikin dokar.
Sabon sashe na 8 ya bayyana cewa duk wanda aka samu a cikin jam’iyyu biyu a lokaci guda ba za a yi masa rajistar zama ɗan jam’iyya ba.
Sashe na 9 kuma ya ce idan aka gano mutum yana cikin jam’iyyu biyu a lokaci guda, za a soke rajistar duka jam’iyyu biyun nan take.
Sai kuma sashe na 10 wanda ya tanadi cewa duk wanda da gangan ya yi hakan, ya aikata laifi da zai iya jawo masa ɗaurin shekara biyu a gidan yari.
Hakazalika, sashen ya bayar da zaɓin biyan tarar Naira miliyan 10, ko kuma a haɗa masa hukuncin duka biyun.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link