An naɗa Benjamin Hundeyin sabon kakakin ’yan sandan Nijeriya

[ad_1]



Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, IGP Kayode Egbetokun, ya amince da naɗin CSP Benjamin Hundeyin a matsayin sabon Kakakin ’Yan Sanda na Ƙasa (FPRO).

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar mai barin gado, Muyiwa Adejobi ya fitar.

Kafin sabon muƙamin, CSP Benjamin Hundeyin ya kasance kakakin rundunar ’yan sanda reshen Jihar Legas, inda ya kwashe shekaru yana wannan aiki.

Hundeyin ya yi karatu a fannin Turanci da kuma nazari da halayyar masu laifi da tsaro wato Criminology da Security Psychology.

Haka kuma, memba ne na ƙungiyoyin ƙwararru kamar Nigerian Institute of Public Relations (NIPR) da International Public Relations Association (IPRA).

A shekarar 2020 kuma ya kasance cikin tawagar Najeriya a aikin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a Darfur, Sudan.

Sufeto Janar ɗin ya buƙaci sabon kakakin da ya yi amfani da ƙwarewarsa wajen inganta ayyukan rundunar da kuma ƙarfafa hulɗa a tsakanin ‘yan sanda da al’umma.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *