Ma’aikatar Wajen Sin Ta Maida Martani Kan Mummunan Harin Bam Da Aka Kai Pakistan

[ad_1]

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya amsa tambayar manema labarai a yau Lahadi 8 ga watan Fabrairu, dangane da mummunan harin bam da aka kai a birnin Islamabad na kasar Pakistan.

An samu mummunan tashin bam da maraicen ranar 6 ga wata a birnin Islamabad, al’amarin da ya jawo babbar hasarar rayuka. Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce, Sin ta kadu matuka game da aukuwar wannan mummunan harin bam wanda ya haddasa babbar hasarar rayuka, tare da nuna matukar alhini kan wadanda suka rasa rayukansu, da isar da sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan gami da wadanda suka ji rauni.

Jami’in ya kara da cewa, Sin ta yi Allah wadai da wannan harin ta’addanci, da nuna adawa da duk wani nau’in aikin ’yan ta’adda, tare da nuna wa gwamnatin kasar Pakistan cikakken goyon-bayan wurin tabbatar da zaman lafiyar da kwanciyar hankali gami da kare tsaron al’umma. (Murtala Zhang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *