El-Classico: Real Madrid Ta Duke Barcelona Da CI 2




Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta doke babbar abokiya hamayyarta, Barcelona da ci 2 da 1 a filin wasa na Bernabeau.

Wasan tsakanin manyan ƙungiyoyin biyu shi ne wasa mafi girma na hamayya a duniya.

Madrid ta karɓi baƙuncin Barcelona a gasar Laliga a wasan mako na 10.

Wasan ya ƙayatar, inda kowace ƙungiya ta nuna bajinta tare da murza leda yadda ya kamata.

Ɗan wasan gaban Real Madrid, Kylian Mbappe ne ya fara jefa ƙwallo a minti na 22, yayin da Fermin Lopez ya warware wa Barcelona a minti na 38.

Kafin tafiya hutun rabin lokaci, ɗan wasan tsakiyar Real Madrid, Jude Bellingham, ya sake jefa mata ƙwallo ta biyu a raga, a minti na 43.

Yanzu haka Madrid na ci gaba da jan ragamar teburin gasar da maki 27 daga wasanni 10, inda ta lashe wasa tara ta kuma yi rashin nasara a wasa ɗaya.

Barcelona kuwa, tana mataki na biyu da maki 22 daga wasanni 10, inda ta yi rashin nasara a wasanni biyu, tare da yin kunnen doki a wasa ɗaya.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *