Yara sun gano harsasan bindigar jirgin sama a Maiduguri

[ad_1]



Wani abin mamaki ya faru a unguwar Bulunkutu da ke Maiduguri, Borno, inda yara ƙanana da ke kamun kifi a magudanar ruwa suka gano tarin harsashin bindigar jirgin sama da ke da rai.

Rahotanni daga yankin sun ce ana zargin ’yan Boko Haram ne suka ajiye waɗannan harsasai kafin su gudu.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa bayan da yaran suka lura da abubuwan da ba su saba gani ba, sai suka sanar da hukumomi. Wannan ya sa dakarun soji suka gaggauta kakkabe yankin.

Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa, “Yaran duk ƙanana ne, babban cikinsu bai wuce shekara 13 ba. A kullum suna kamun kifi idan ruwa ya fara raguwa. Amma wannan karon, maimakon kifi sai suka ciro harsasai da yawa tare da wasu ‘power bank’, abin da ya tayar da hankalin jama’a.”

Ya kara da cewa jami’an tsaro – sojoji, ’yan sanda da CJTF – sun gudanar da bincike a yankin.

Malam Bishir, wani mazaunin unguwar, ya ce, “Abin da ya fi damun jama’a shi ne tarihin wannan wuri. A da wasu manyan ’yan Boko Haram sun zauna a nan kafin CJTF su kore su.

“Mutane na ganin waɗannan harsasai su ne suka bari, shi ya sa kowa ke cikin fargaba musamman a kusa da masallatai.”

Wani bidiyo da ya kalla ya nuna yara 11 zaune a ƙasa, ana yaba musu tare da karɓar kyautar kuɗi daga jami’an tsaro na Sector 9 saboda irin kulawarsu.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake cikin tsananin fargabar tsaro a Borno da maƙwabtan jihohin Yobe da Adamawa, inda aka samu fashewar bama-bamai da kuma yunƙurin kai hare-haren ƙunar bakin wake a ’yan makonnin nan.

A baya-bayan nan, dakarun Operation HADIN KAI (OPHK) sun kama wanda ake zargi da kitsa harin bama-bamai a Maiduguri, wanda ya hallaka mutane biyar tare da jikkata wasu 34 a cikin masallaci.

Kakakin rundunar, Laftanar-Kanar Sani Uba, ya bayyana wanda aka kama, Sheriff Umar, a matsayin babban mai tsara hare-haren ƙunar bakin wake da suka shafi hare-haren baya-bayan nan a shiyyar Arewa maso Gabas.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *