Ramadan: Zulum Ya Raba Wa Magidanta 300,000 Kayan Abinci A Borno

[ad_1]

Gwamna Babagana Umara Zulum, ya raba kayan agajin watan Ramadana ga magidanta kimanin 300,000 na Musulmi da Kirista a fadin kananan hukumomi 27 na Jihar Borno.

Da yake kaddamar da rabon kayan abincin a Maiduguri, Zulum ya ce; an dauki wannan mataki ne, don rage wahalhalun tattalin arziki da mazauna karkara ke fuskanta a halin yanzu.

  • Iyayen Marayu 501 Ne Suka Samu Tallafin Abincin Azumi Daga Dan Amo A Kano
  • Sin Ta Ba Da Shawarar Tsayawa Kan Ra’ayoyin Bai Daya Guda Biyar Don Warware Rikicin Sudan

Ya lura cewa, lokacin Azumin Kirista, ya zo daidai da watan Ramadana na wannan shekarar, yana mai jaddada cewa; gidajen Kiristoci, su ma za su amfana da wannan rabo na kayan abinci.

A cewar gwamnan, kowane mai cin gajiyar, zai samu buhun shinkafa, buhun gero da kuma kilo 10 na sikari.

Ya kara da cewa, an ware dubban buhun shinkafa, gero da sikari, domin rarrabawa ga tsofaffi mazauna jihar.

Zulum ya bukaci membobin kwamitin rarrabawar, da su tabbatar da gaskiya da adalci a cikin wannan tsari.

“Wadannan kayan, ba na sayarwa ba ne. Ba an yi su ne don abokanka ko ‘yan’uwanka wadanda ba sa bukatarsu ba,” in ji shi.

“An tanade su ne domin zawarawa da marayu da wadanda aka kora daga matsugunansu da manoma wadanda gonakinsu ba su yi cikakkiyar farfadowa ba da kuma wadanda ke fama da matsalar biyan albashi a kullum. Duk wani jami’i da aka samu yana karkatar da wadannan kayayyaki, zai fuskanci fushin doka.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *