Babu abin da aka sauya a cikin sabbin dokokin haraji — Akpabio

[ad_1]



Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya musanta iƙirarin cewa an sauya sabbin dokokin haraji bayan Majalisar Tarayya ta amince da su.

Ya ce dokokin da Shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu kuma aka wallafa a jaridar gwamnati su ne waɗanda ’yan majalisa suka amince da su.

Akpabio, ya bayyana haka ne bayan wani ɗan Majalisar Tarayya, Abdussamad Dakuku, ya ce dokokin harajin da aka fitar sun bambanta da waɗanda majalisa ta amince da su.

Sai dai Akpabio ya ce wannan iƙirari ba shi da tushe, inda ya jaddada cewa takardun da Majalisar Tarayya ta tabbatar ne kaɗai sahihai.

“Ina sane da cewa akwai wani salo da ke yawo, wanda bai dace da bayanan zaman majalisa ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “Babu wani sauyi ko cushe ko kaɗan a cikin dokokin da shugaban ƙasa ya sanya wa hannu.”

A cewarsa, dokoki huɗu na gyaran haraji sun samu amincewar shugaban ƙasa, sannan aka tabbatar da su ta hannun Magatakardar Majalisar Tarayya.

Ya umarci Magatakardar Majalisar Dattawa da ya raba kwafin dokokin da aka tabbatar ga dukkanin Sanatoci, tare da gargaɗin kada a riƙa fitar da su ta hanyoyin da ba na hukuma ba domin kauce wa yaɗa jita-jita da bayanan ƙarya.

A wani ɓangare kuma, Majalisar Dattawa ta ɗage tattauna rahoton Kwamitinta kan Harkokin Zaɓe domin bai wa Sanatoci ƙarin lokaci domin su nazarci rahoton.

Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce an ɗage zaman ne saboda rashin halartar shugaban kwamitin, Simon Lalong.

Akpabio, ya goyi bayan ɗagewar, yana mai cewa majalisa ta fi son yin aiki cikin taka-tsantsan sama da yin gaggawa.

“Ba ma buƙatar yin gaggawa kan wannan rahoto; bin ƙa’ida da adalci ne za su jagoranci matakin majalisar nan,” in ji shi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *