Akpabio: Ba A Canza Komai A Cikin Sabbin Dokokin Haraji Ba

[ad_1]

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ƙaryata zargin cewa an sauya sabbin dokokin haraji bayan Majalisar Tarayya ta amince da su.

Ya ce dokokin da Shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu kuma aka wallafa a jaridar Gwamnatin Tarayya dai-dai suke da abin da ’yan majalisu suka amince da su.

  • Raheem Sterling Ya Bar Chelsea Bayan Shafe Shekaru 3
  • Firaministan Kasar Birtaniya Zai Ziyarci Kasar Sin

Akpabio ya bayyana hakan ne bayan wani ɗan Majalisar Wakilai, Abdussamad Dakuku, ya yi iƙirarin cewa dokokin harajin da aka fitar sun bambanta da waɗanda majalisar ta amince da su.

Shugaban Majalisar Dattawan ya ce wannan iƙirari ba gaskiya ba ne.

Ya jaddada cewa duk wata doka da ba Majalisar Tarayya ce ta fitar da ita kuma ta tabbatar da ita ba, ba za a ɗauke ta a matsayin sahihiya ba.

A cewarsa, an tattauna dokokin harajin sosai a Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai, sannan aka daidaita duk wani abu kafin a tura su zuwa wajen shugaban ƙasa.

“Babu wani canji ko sauyi da aka yi wa dokokin da aka sanya wa hannu,” in ji shi.

Akpabio ya bayyana cewa dokoki huɗu da suka shafi haraji sun kammala bin dukkanin matakan dokoki.

Ya ce ’yan majalisu sun amince da dokokin, sannan Shugaba Tinubu ya sanya musu hannu, sannan aka wallafa su a hukumance.

Don kauce wa ruɗani, Akpabio ya umarci Magatakardar Majalisar Dattawa da ta raba sahihan kwafin dokokin ga dukkanin sanatoci.

Ya kuma yi gargaɗi cewa kada a riƙa fitar da dokokin ta hanyoyin da ba na hukuma ba, domin hakan yana haifar da jita-jita da yaɗa bayanan ƙarya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *