Manyan Nasarorin Da Dr Matawalle Ya Samar A Sashen Tsaro

[ad_1]

Daga Bashir Aliyu

Tun da aka nada shi a matsayin Karamin Ministan Tsaro a 2023, Dr Bello Matawalle ya sake kawo sabon dabaru ta fannin tsaro, nazari da kuma daukar matakan da suka jibi dasa tubalin ginin sashen tsaro na kasa. A lokacinsa an samu manyan nasarori a bangaren yaki da ta’addanci, zamanantar da rundunar soja, da kuma tabbatar da zaman lafiyar kasa, wadanda ne suka sa ake kallonsa a matsayin daya daga cikin manyan mutunen da suke bayar da muhimmiyar gudummawa wurin yaki da rashin tsaro.

A lokacin jagorancinsa ne Ma’aikatar Tsaro ta samu manya-manyan nasarori domin kawo zaman lafiya a kasa. Wadannan nasarori su ne:

Nasarori A Kan Ta’addanci Da Satan Mutane

Daya daga cikin manyan nasarorin da Dr Bello Matawalle ya samu shi ne kaimi da aka yi wurin yaki da ta’addanci. Ta hanyar kyautata hadin gwiwa da Sojojin kasa, da Sojojin Sama da sauran hukumomin tsaro, an yi rugu-rugu da matattaran ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas, wanda hakan ya yi sanadiyar raguwar hare-hare. A Arewa Maso Yamma kuwa, gagarumar gudummawa da ma’aikatar tsaro a karkashinsa ta amfani da karfin soja ya yi mummunar illa ga matattarar ‘yan ta’adda wanda hakan ya kyautata fata da al’umma ke da shi cewa an kusan share musu hawaye.

Kula Da Walwalar Sojoji Da Karfafa Musu Gwiwa

Ganin cewa karfin Sojan Nijeriya ya dogara ne a rundunarta, Dr Bello Matawalle ya inganta hanyoyin walwalar sojojin ta hanyar biyan su kudin alawus a kan lokaci, kyautata matsuguninsu, da kuma samun ingantaccen kiwon lafiya. Wannan ya kara azama wa sojojin da suke gwabza yaki a fagagen fama.

Zamanantar da Dakarun Sojoji

Ganin bukatar gaggawa da ke akwai na zamanan tar da sojojin Nigeriya, Dr Bello Matawalle ya samar da waraka ta hanyar samar da sabbin makamai na zamani, da jirage marasa matuki don tattara bayanai da kuma kayan ayyuka da sojoji ke bukata lokacin yaki.

Wadannan kayayyaki sun inganta dabarun da sojoji ke amfani da su ta hanyar raguwar yawan sojojin da ke rasa rayukansu da kuma karuwar nasarori a duk lokacin da aka fita ba-ta-kashi.

Raguwar sace-sacen mai da zagon kasa wa tattalin arziki.

Tattalin arzikin Nijeriya ya jima na fama da yawan watan danyen mai a yankin Niger Delta.

Karkashin jagorancin Matawalle, an samu karuwar aikace-aikacen da suka hada da hadin gwiwar sojojin ruwa wadanda suka hada da lalata cibiyoyin sace danyen mai wanda hakan ya haifar da karuwar danyen mai da ake fitar da kuma karin kudaden shiga ga kasa.

Karfafa mu’amala da hadin gwiwa da kaware a yankin Africa da kasa-da-kasa.

Yawancin matsalolin tsaro ya kan wuce iyakar kasa, saboda haka ne Dr Matawalle bai yi kasa a gwiwa ba wurin daukar matakan kulla kawance da makwabtan kasashe irin su Chad, da Niger da Kamaru, da sauran kawayen kasashe irin su Amurka, Birtaniya da Tarayyar Turai wanda ya inganta yanda ake tattara bayanai da kuma musayar bayanan sirri. Hakan ya sa ‘yan ta’adda da masu aikata muggan laifuka ke samun wahalar samun maboya.

Karfafa kere-keren kayan yaki a gida

Bisa umurnin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar na tunanin dogaro da Kai a fannin tsaro, Dr Bello Matawalle ya yi kokarin agaza wa Hukumar Samar da Kayan Yaki ta Nijeriya (DICON) domin kara samar da makaman yaki a gida Nijeriya. Wannan mataki ya rage dogaro da kasashen waje da kuma karfafa tattalin arzikin tsaron Nijeriya.

Baya ga bangaren yaki, Dr Bello Matawalle yana cigaba da jaddada muhimmancin aiki da al’umma domin dawo da tsaro. Wannan kiranye da yake yi wurin neman tattaunawa, da sasanci da kuma ayyukan ci gaba a yankunan da ake rikici sun taimaka matuka gaya wajen dinke rashin yarda tsakanin jami’an tsaro da kuma fararen hula, wanda hakan zai haifar da zaman lafiya mai dorewa.

Jagorancin Dr Bello Matawalle ya nuna aiki ba kama kafar yaro, sabbin dabaru, da kuma kishin kasa. Nasarorinsa ya nuna irin fahimtarsa a matsalolin tsaron Nijeriya da kuma irin niyyar da gwamnati ke da shi wurin magance su.

Bashir Aliyu dan jarida ne mai nazarin al’amuran da suka shafi siyasa da tsaro.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *