HOTUNA: An sake gano harsasai masu rai a Maiduguri
[ad_1]
An sake gano wasu harsasai masu rai a yankin Kumshe da ke Maiduguri da ke Maiduguri, kwanaki kaɗan bayan sojoji suka bankado wani babban rumbun makamai da ake zargin na mayakan Boko Haram ne a yankin a Bulumkutu da ke garin.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai cewa jami’an ’yan sanda da na rundunar haɗin gwiwa ta Sibiliyan JTF sun kasance a wurin da aka gano harsasan, kusa da layin jirgin ƙasa, har zuwa ranar Lahadi.
“’Yan sanda da CJTF sun tabbatar da tsaron yankin. Jami’an da ke kula da bama-bamai suna ci gaba da bincike a wurin,” in ji majiyar.
Kumshe na da tarihin alaƙa da ayyukan ta’addanci, kasancewar yana kusa da Markas, tsohon hedikwatar marigayi shugaban Boko Haram, Mohammed Yusuf.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta sanar da cewa ta yi nasarar kama harsasan da aka gano a wani samame, kuma tana ci gaba da bincike domin gano asalinsu da kuma yadda aka yi amfani da su, tare da kama waɗanda ke da hannu a ciki.
Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana cewa Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Naziru Abdulmajid ya yaba wa jama’a bisa bayanan da suka bayar cikin lokaci, wanda ya taimaka wajen nasarar da aka samu.

Ya kuma nanata cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa jagorancin leken asiri da tsare-tsare na musamman.
ASP Daso ya ƙara jaddada kira ga mazauna yankin da su ci gaba da haɗa kai da ’yan sanda ta hanyar bayar da rahoton duk wani abu da ake zargi ko ayyukan da ake aikatawa a cikin al’ummominsu cikin gaggawa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link