Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Amsa Tambayoyin Manema Labaru
[ad_1]
Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, zai kawo ziyarar aiki kasar Sin tsakanin ranekun 25 zuwa 26 ga Fabrairu. Yayin da take bayani a kan ziyarar a taron manema labarai na yau Talata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning, ta bayyana cewa, wannan ziyara ita ce ta farko da Mr. Merz zai kawo kasar Sin tun bayan rike mukaminsa. Ta kara da cewa, a lokacin ziyarar, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gana da shi, kuma firaministan kasar Li Qiang shi ma zai tattauna da shi, inda za su yi musayar ra’ayoyi kan dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, da wasu batutuwan dake jan hankulansu duka. Kakakin ta kuma ce, “A matsayinsu na kasa ta biyu da ta uku mafi karfin tattalin arziki a duniya, ciyar da dangantakar dake tsakanin Sin da Jamus gaba yadda ya kamata, ta dace da muradun bangarorin biyu da kuma fatan duniya.”
Hakazalika, game da tambayar da aka yi game da martanin kasar Sin kan labarin da aka bayar cewa shugaban kasar Amurka Donald Trump zai kawo ziyarar aiki kasar a karshen watan Maris zuwa farkon watan Afrilu. Mao Ning ta ce, diflomasiyyar shugabannin kasashen biyu tana taka muhimmiyar rawar da ba za a iya maye gurbinta ba wajen jagorantar dangantakar Sin da Amurka bisa manyan tsare-tsare, kuma bangarorin biyu na ci gaba da tuntubar juna kan batun ziyarar shugaba Trump a kasar Sin.
Da aka tambaye ta game da rikicin Ukraine, Mao Ning ta ce, an bude kofar tattaunawa kan rikicin Ukraine a kwanan nan, kuma tattaunawa da shawarwari hanya ce daya tilo da za a bi don magance rikicin, kakakin ta bayyana fatanta na ganin bangarori daban daban su yi amfani da damar don cimma yarjejeniyar zaman lafiya mai karfi da dorewa daga dukkan fannoni. (Bilkisu Xin)
[ad_2]
Source link