Sin Ta Bukaci Amurka Ta Dakatar Da Matakan Kakaba Haraji

[ad_1]

Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin ta bayyana a yau Talata cewa, kasar na adawa da duk wani nau’i na matakan kakaba haraji daga bangare guda, tana mai kira ga Amurka ta soke ta kuma kauracewa kakaba haraje-haraje.

A martaninsa game da tambaya kan batun karin harajin kaso 10 daga Amurka da kuma nuna cewa za ta sake kara haraji bisa dogaro da sassa na 301 da 232 na bincike, kakakin ya ce kasar Sin tana bibiyar matakan Amurka game da batun. Sannan za ta yanke shawarar da ta dace game da matakan martani dangane da batun harajin da ya shafi fentanyl, da haraje-harajen ramuwa. Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta dage wajen kare hakkoki da muradunta na halal.

Bugu da kari, kakakin ya ce a shirye Sin take ta yi tattaunawa bisa gaskiya tsakaninta da Amurka yayin zagaye na 6 na tattaunawar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu dake karatowa, kuma tana fatan Amurka za ta rike matsayar da aka cimma yayin ganawar da shugabannin kasashen biyu suka yi a Busan da kuma tattaunawa ta wayar tarho da suka yi a ranar 4 ga watan Fabrairu. (FMM)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *