Kasar Sin Ta Sanya Wasu Kamfanonin Japan Karkashin Kayyadewar Tsarin Sa Ido A Fannin Fitar Da Kayayyaki
[ad_1]
A yau Talata, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta sanar da sanya wasu kamfanonin kasar Japan guda 20 cikin jerin kamfanonin da ake sanya musu ido a fannin fitar musu da kayayyaki daga kasar Sin.
Ma’aikatar ta ce, bisa dokokin kasar Sin masu alaka da fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare, kuma a bisa zummar tabbatar da tsaron kasar da moriyarta, da sauke nauyin magance bazuwar makamai a duniya, ta yanke shawarar sanya kamfanin kera jiragen ruwa na Mitsubishi na kasar Japan, da sauran kamfanonin kasar 19, wadanda dukkansu ke samar da taimako ga kasarsu wajen kara karfin sojanta, cikin jerin kamfanonin da ake sanya musu ido a fannin samun kayayyakin da ake fitarwa daga kasar Sin.
Ban da haka, duk a yau Talata, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta sanya sauran wasu kamfanonin kasar Japan 20, ciki har da kamfanin Subaru, wadanda aka kasa tabbatar da ko suna ba da taimako wajen kara karfin soja na kasar Japan, cikin jerin kamfanonin da ake mai da hankali kan ayyukansu.
A cewar ma’aikatar, ta gabatar da matakan ne don hana kasar Japan sake zama wata kasa mai cikakken karfin soja, da yunkurinta na neman samun makaman nukiliya, inda matakan suka nuna adalci, da yanayin dacewa da doka. Bugu da kari, ma’aikatar ta ce matakan da bangaren Sin ke dauka sun shafi kalilan kamfanonin kasar Japan, da kayayyaki masu alaka da aikin soja ne kawai. Ba za su haifar da tasiri kan cudanyar tattalin arziki da cinikin da ake yi tsakanin bangarorin Sin da Japan ba. Saboda haka, kar kamfanonin kasar Japan masu bin doka su damu sakamakon batun. (Bello Wang)
[ad_2]
Source link