Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alƙawarin Kawo Ƙarshen Matsala Tsaro A Zamfara

[ad_1]

Gwamnatin Tarayya ta jaddada alkawarin kawo ƙarshen matsalar Tsaro daya ki ci yaki cinyewa a Jihar Zamfara da jihohin dake fama da matsalar a arewa maso yamma da sauran jihohi.

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shatima ya bayyana haka a Bikin Bada Tutar Jam’iyyar APC ga Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal daya gudana a Kasuwar Bajekoli dake Gusau, babban birnin Jihar a yau Talata.

  • Manufar Kasar Sin Daya Tak A Duniya Ita Ce Tushen Siyasa Ta Shigar Taiwan Ayyukan WTO
  • NPC Ta Yi Rajistar Haihuwa 36,000 A Kano Cikin Watanni 9

Sanata Kashin Shatima ya bayyana cewa, komawar Gwamna Dauda APC za a samu gagarimar nasara da cigaban al’ummar Jihar Zamfara da Kasa baki daya.

Kuma yakawo hadin kan Jamiyyar APC a fadin Jihar ta Zamfara, domin yanzu haka, Jamiyyar PDP an yi jana’izar ta, ita kuma Jam’iyyar ADC bata da gurbi a Jihar ta Zamfara.

A nasa jawabin, gwamna Dauda Lawal ya tabbatar da cewa, zai tafi da ‘yan Jam’iyyar baki daya babu wani banbanci a tsakanin ‘yar Jamiyyar.

Gwamna Dauda ya kuma dau Alwashin cigaba da ayyukan more rayuwa ga al’ummar Jihar Zamfara kamar yadda yake gabatarwa a yanzu haka.

Anasu jawaban Tsafin gwamnonin Jihar Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari da Ministan Tsaro, Bello Matawalle su bayyana murnar su da godiya ga Allah da gwamna Dauda Lawal ya dawo cikin dangi.

Kuma sun tabbatar da cewa, babu wani dan takara a Shekara ta 2026 na gwamnan a Zamfara, sai gwamna Dauda Lawal

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *