Isra’ila Ta Ƙaddamar Da Hare-Hare Kan Iran Da Lebanon
[ad_1]
Isra’ila ta sanar da ƙaddamar da abin da ta kira harin “kariya” kan Iran, yayin da shaidu suka ruwaito jin ƙarar fashe-fashe a birnin Tehran da safiyar Asabar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Haka kuma jiragen yaƙin Isra’ila sun kai hare-hare a yankunan Blat da Wadi Barghouti na kudancin Lebanon, da a Iqlim al-Tuffah, lamarin da aka bayyana a matsayin sabon karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a Nuwamban 2024 tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah.
- Hare-haren Isra’ila Ta Sama Ya Kashe Falasɗinawa 11 A Gaza
- Sin Na Bibiyar Halin Da Ake Ciki Yayin Da Zaman Tankiya Ke Karuwa Tsakanin Amurka Da Iran
Sojojin Isra’ila sun ce hare-haren an ki su ne kan cibiyoyin Hezbollah a kudancin Lebanon, sai dai rahotanni sun nuna cewa hare-haren da ake kai wa kusan kullum na shafar fararen hula da muhimman ababen more rayuwa.
Tashar Al-Mayadeen ta Lebanon ta tabbatar da cewa jiragen yaƙin Isra’ila sun kai hare-hare kan tsaunukan al-Tuffah, yayin da Al-Manar TV ta Hezbollah ta ce jiragen ƙanana marasa matuƙi sun jefa abubuwan fashewa a garin Markaba karo na uku.
A wani hari da aka kai a kwarin Bekaa ranar Alhamis, mutum guda ya mutu yayin da 29 suka jikkata, inda Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon ta ce wani matashi ɗan Syria mai shekara 16, Hussein Mohsen al-Khalaf, ya rasa ransa a Kfar Dan kusa da Baalbek.
[ad_2]
Source link