Kusan Shugabannin Kamfanoni 100 Ne Suka Taru Domin Halartar Dandalin Bunkasa Kasar Sin
[ad_1]
A baya-bayan nan, yayin taron dandalin bunkasa kasar Sin na shekarar nan ta 2026, wanda ya gudana a birnin Beijing, kusan shugabannin kamfanoni 100 sun taru, domin tattauna dabarun hadin gwiwa cikin harabar gudanar da taron. A wajen dandalin gudanar da taron kuwa, manyan jami’an kamfanonin kasa da kasa sun ziyarci ma’aikatar cinikayyar Sin, da ma wasu karin ma’aikatu da cibiyoyin gwamnati, suna masu amfani da damar hakan wajen tattaunawa, a gabar aiwatar da shirin raya kasar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 15 na Sin. Masu zuba jari na ketare, sun sha maimaita batun shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15, kasancewar hakan ya fayyace sabuwar taswirar bunkasa kasar Sin, baya ga sabuwar damar da hakan zai samar ga ci gaban duniya baki daya. Tabbacin da manufofin gwamnatin kasar Sin ke da shi, ya baiwa kamfanoni masu jarin waje zarafin tsara ayyuka cikin nutsuwa zuwa tsare-tsare na dogon zango. Babbar kasuwar Sin mai farfadowa, ta samarwa kamfanonin kasashen duniya daban daban da damammakin cimma moriya tare. Daga watan Janairu zuwa Fabrairun bana, Sin ta kafa sabbin kamfanoni masu jarin waje 8,631, matakin da ya nuna karuwar kaso 14 bisa dari a mizanin shekara-shekara. Kamfanoni masu jarin waje sun yi amannar cewa, “Zuba jari a Sin zuba jari ne domin gobe”. Duk da karuwar daukar matakan kashin kai da kariyar cinikayya, sassan dake neman bunkasa hadin gwiwa, da goyon bayan ci gaba na kara bunkasa. Har ila yau, ana samun karin gudanar da harkoki a bude, da hadin gwiwa, da cimma moriyar bai daya, matakan dake zamowa karbabbu a zamanin yanzu. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link