Budaddiyar Wasika Ga Gwamnan Kano Abba K. Yusuf
[ad_1]
Wannan budaddiyar wasika, na kunshe ne da wasu shawarwari masu alfanu, don maigirma gwamna ya yi wukar gindi da su, cikin sabuwar jam’iyyar APCn da ake sa-ran zai koma ba da dadewa ba.
Babu shakka kamar yadda yake faruwa a akasarin jihohi, magoya bayan jam’iyyar APC a Kano ma, na da irin nasu banbance-banbancen ra’ayoyi a jam’iyyar. Sai dai hakikanin gaskiya, sabanin ra’ayoyin siyasa a yau, sun banbanta da na-dauri. Saboda a lokutan da suka shude, a na yin jagorancin siyasa ne, ko na gwamnati kadai, don hidimtawa ga al’umma, ba domin a wawashe dukiyar jama’ar kasa ba!.
Duk da mummunan sabanin siyasar da ya afku tsakanin marigayi Malam Aminu Kano, da marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi, wanda har ya kai ga salwantar rayuka da dukiyoyi, babu wanda zai bugi kirji a Kano cewa, sun yi wancan sabanin ne, a kan hanyarsu ta wawashe dukiyar jama’ar Kano. Tarihi shaida ne, wadannan hamshakan jagororin siyasa biyu (Rimi da Malam) a Kano, sun fi karfin tarihin siyasar jihar ya sanya su cikin kwandon shara, duba da irin gagarumar gudunmuwar da suka bayar wajen “yantar da raunanan mutane daga azzaluman shugabanni, masu wawashe musu dukiya, tare yi musu dadin-baki. Sabanin akasarin jagororin siyasar yau, wadanda suka kware wajen farfaganda da kawo mummunan rudani a tsakanin “yan jam’iyya. Bugu da kari, ga su manyan beraye ne irin na dinka, a duk sa’adda suka sami damar darewa bisa madafun iko da kansu, ko suka sami damar dora wani yaronsu, a ko da yaushe, sun fi so a bar musu akushin baitul malin al’uma su sarrafa shi son-ransu, sabanin haka kuwa, za su cika gari da babatun an butulce musu. Wata shari’ar kam sai a Lahira!!!.
Mabanbantan Gidajen Akidun Siyasa A APCn Kano
Maigirma gwamna, batun banbancin gidajen akidun siyasa a Kano kuwa, wani al’amari ne da ya samo asali ne tun daga Jamhuriyar Siyasa ta farko a wannan kasa. Lokacin da jam’iyyun NPC da NEPU suka yi walle-walle a tsakani. Wancan sabani da ya faro daga farkon tarihin siyasar kasar, shi ne ya yi naso har zuwa Jamhuriyar Siyasa ta biyu, inda zazzafan sabanin ra’ayi ya sake barkewa a tsakanin jam’iyyar NPN (gyauron NPC) da ta PRP (gyauron NEPU) a jihar Kano. Wannan sabani, ya bayu har zuwa ga asarar rayuka da dukiyoyi.
Jamhuriyar Siyasa ta uku kuwa, ta zo ne lokacin Soja, karkashin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), inda gwamnati ta samar da jam’iyyun siyasa biyu rakkin, NRC da SDP. Nan ma, sai birbishin ayarin tsohuwar jam’iyyar PRP suka fi karkata ga SDP, su kuwa birbishin jam’iyyar NPN sun rankaya ne zuwa NRC. Daga lokaci zuwa lokaci, gidajen siyasa a Kano suka rika yaduwa har kawo yau (2026). Sai dai, wani dalili ya sanya su rikidewa zuwa wani abu daban a wannan lokaci.
Rikedewa Daga Akidar Siyasa Zuwa Son-rai
A farko-farkon wannan Jamhuriyar Siyasa ta hudu a Kano karkashin jagorancin jam’iyyar PDP, wadda ta fara a Shekarar 1999, sanannun gidajen siyasa hudu (4) ne a Kano, wanda kowane gida akwai madugunsa: akwai gidan NPN, wanda Ambs. Aminu Wali ke jagoranta. Akwai gidan Santsi, wanda marigayi Muhammadu Abubakar Rimi ke shugabanta. Sannan akwai gidan Tabo, wanda mutane irin su marigayi Dangalan da marigayi Musa Gwadabe ne ke jan linzaminsa. Amma a yau, ba haka zancen yake ba.
Wanda ke bibiyar motsin siyasar Kano karkashin wannan jamhuriya ta hudu, ya kwana da sanin cewa, tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, kusan shi ne dan siyasa a Kano mafi tasiri, wajen farauto “ya”yayen da yawa daga mabiya wadancan gidajen siyasa uku (3), tare da cin-ganimarsu. Bugu da kari, a kullum Kwankwason, yakan nuna inganta rayuwar matasan ne a gabansa. Ko da yake, tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau da ya gaje kujerar gwamnan daga Kwankwaso, shi ma ya wafci nasa kason mutane daga wadancan gidajen akidu uku na siyasa. Wasu mutanen ma da Shekarau ya wafta, sun kasance suna tare da Kwankwaso ne a lokacin da ludayinsa ke kan dawo (lokacin da yake gwamna), yana barin iko, sai suka sauya sheka nan take.
Maigirma gwamna, an wayigari a yau, karsashin wanzar da tsantsar akidar siyasa ta gaskiya, tuni ta fice daga zukatan sama da kashi casa’in da biyar (95%) na “yan siyasa. Babban abin la’akari a yau shi ne, mutum ya samu sukunin darewa bisa kujerar mulki, koko ya zo da madarar kudinsa, nan da nan ne zai sami magoya baya. Wanda ya tabbata a zahiri, kujerar gwamna ce ta taka rawa, wajen bai wa Sanata Kwankwaso damar hada sansanin siyasa a karkashinsa. Haka tsoffin gwamnoni a bayansa, Shekarau da Ganduje, suma sun sami nasarar kafa sansaninsu na siyasa ne, saboda ni’imar kujerar mulki da suka dosana. A lokutan siyasar baya ne ake tara magoya baya masu sahihiyar akidar siyasa, ko da kuwa babu kudi babu mulki, amma ban da wannan lokaci da ake ciki. Mai yi wa, hakan ba ya rasa nasama da hali na madarar talauci da aka tsinci kai ciki, uwa uba ma ga rashin Ilimi.
Sansanonin Siyasar Ganduje Da Barau
Kamar yadda maigirma gwamna ya sani cewa, yau a Kano cikin jam’iyyar APCn da ake rade-radin zai koma, akwai wasu manyan rundunoni biyu na siyasa: tawagar Ganduje da ta Barau. Wadanda tsawon lokaci suke hararar juna, musamman wajen ganin waye cikinsu zai sami tikitin zama dan takarar kujerar gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar. Sai dai zuwa yanzu, wajibinsu ne mayar da wuka cikin kube, domin kuwa kai ne wanda a yau tsarin mulkin jam’iyyar zai danka jagorancin jam’iyyar sukutun a hannunka.
Ba ya ga Kwankwaso da Shekarau da Ganduje, shi ma Sanata Barau ya rabauta da irin nasa tarin magoya baya a yankin Kano ta Arewa, da ma daukacin sasannin Kano bakidaya, duba da irin taragon arziki da ya jima yana saukewa al’umma.
A Inda Gizo Ke Sakar…
Yaya halayen Ganduje da zugarsa suke? Yaya halayen Barau da zugarsa suke?. Sanin halayyar mabanbantan wadannan sansanoni biyu, na da gayar muhimmanci gare ka. Duk da ka fi su karfin magoya baya a Kano, akwai wasu wurare da wasunsu za su iya yi maka illa, musamman wajen dora su bisa wakilci, ba tare da a na bibiyarsu ba.
A karshe, maigirma gwamna, a yi la’akari da wasu shawarwari kamar haka;
1- A ci gaba da kwararo wa Kano ayyukan alheri, ta hanyar haka ne za kai galaba akan magautan fili da na boye, daga kowace jam’iyya ne suke.
2- A fi mayar da hankali bisa aiki, abar magauta su yi ta tsiyaya ka da a biye musu.
3- A tallafi matasa, tallafi mamako.
4- A tallafa wa mata, tallafi gwaggwaba.
5- Lallai ne a rika bibiyar wadanda aka dorawa amanar isar da sakonnin gwamnati ga al’umma.
b- A rika bibiyar gidajen manyan mutane a jiha, don girmama su tare da amso kyawawan shawarwarinsu.
7- A rika yin kokari, wajen cika alkawuran da aka yi wa jama’a jiya da yau.
8- Wanda aka dankawa mukami ya gaza aikin, a gaggauta neman madadinsa.
9- Wadanda suka yi maka tutsu a yau, ka tuntsirar da su nan take, sabanin haka, za su bi hanyoyin dakile nasararka ne iya-yinsu. Bugu da kari, za su zamto wakilan wadanda ke son ganin bayan gwamnatinka ne a zabe maizuwa (2027).
10- A rika yin la’akari da kyakkyawan tarihin mutane, wajen dora musu wani nauyi.
Maigirma gwamna ma’assalam
[ad_2]
Source link