Sin Na Adawa Da Matakin Da Birtaniya Ta Dauka Na Sanyawa Kamfanonin Sin Takunkumi Bisa Zargin Alakarsu Da Rasha
[ad_1]
Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin a yau 2 ga watan Maris ta bayyana cewa, ma’aikatar harkokin wajen Birtaniya kwanan nan ta sanar da wani sabon zagaye na takunkumi kan Rasha, wanda ya shafi kamfanonin Sin da yawa. Bangaren Birtaniya ya sha daukar matakan sanya kamfanonin Sin cikin jeren sunayen dakatar da kadarorinsu da hana an yi ciniki da su, bisa zargin alakarsu da Rasha. Matakin Birtaniya takunkumi ne na kashin kanta wanda ba shi da tushe a dokokin kasa da kasa, kuma ba a samu izinin MDD ba, kuma bangaren Sin na nuna rashin gamsuwa sosai kuma yana adawa da shi.
Kakakin ya ce, game da rikicin Ukraine, bangaren Sin ya kasance yana kayyade fitar da kayayyaki masu amfanin fararen hula da aikin soja bisa doka, babu wata matsalar da za a hana alakar hadin gwiwa ta yau da kullum tsakanin kamfanonin Sin da na Rasha. Bangaren Sin ya bukaci bangaren Birtaniya da ya gyara kuskuren nan da nan da ya yi, ya janye takunkumin da ya sanya kan wasu kamfanonin Sin, don kiyaye kyakkyawar ci gaban dangantakar Sin da Birtaniya. Bangaren Sin zai dauki matakan da suka dace don kare hakkin kamfanoninsa. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link