An Wallafa Littafi Mai Taken “Nasarar Yaki Da Talauci Karkashin Jagorancin Xi Jinping”
[ad_1]
Kwanan nan, an wallafa littafi mai taken “Nasarar yaki da talauci karkashin jagorancin Xi Jinping” a kasar Sin.
Bayan shiga sabon zamani, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kai ga cimma nasarar fid da al’ummomin kasar daga kangin talauci, matsalar da ta addabi kasashen duniya da dama. Wannan gaggarumar nasara ta gamsar da al’ummar kasar, tare da burge duniya baki daya. Littafin da aka wallafa ya bayyana yadda kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da babban sakatarensa Xi Jinping a matsayin jigo, ya jagoranci al’ummomin kasar wajen kawar da talauci, bisa muhimman abubuwan da suka wakana, da mutanen da suka ba da babbar gudummawa, da ma wadanda suka sa hannu a lamuran.(Lubabatu)
[ad_2]
Source link