Muryar Ayatullah Khamenei

[ad_1]



Gidan Talabijin na ƙasar Iran ya tabbatar da rasuwar matar Jagoran Addinin ƙasar, marigayi Ali Khamenei, wato Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh.

Kafar yaɗa labarai ta Hamshahri ta ruwaito cewa Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh ta samu munanan raunuka tun a ranar farko da Amurka da Isra’ila suka fara kai hare-hare a Iran, inda daga bisani ta rasu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim ya ce Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh, mai shekaru 79, ta yi doguwar suma tun bayan harin da aka kai a ranar Asabar ɗin da ta gabata, da ya yi sanadiyar mutuwar Khamenei.

Tun a baya, rahotanni sun tabbatar da rasuwar Zahra Haddad Adel, matar Mojtaba Khamenei—ɗa ga jagoran addinin, tare da wata surikar jagoran da jikarsa, Zahra Mohammadi Golpayegani, a hare-haren da suka biyo baya.

Rasuwar ta ƙara ɗora hankalin jama’a kan tasirin rikicin da ke ci gaba da ɗaukar rayukan fararen hula a ƙasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *