Amurka da China sun dakatar da harajin da suka ƙaƙaba wa juna

[ad_1]



Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar da za ta tsawaita dakatar da harajin da ya ƙaƙaba wa ƙasar China na tsawon kwanaki 90.

Trump ya sanar da hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social, sa’o’i kaɗan kafin wa’adin farko da ya tsara ya ƙare.

A ɗaya hannun, ma’aikatar kasuwanci ta ƙasar China ta kuma tabbatar da cewa ita ma ta dakatar da ƙarin haraji kan kayayyakin Amurka daga yanzu zuwa tsawon kwanaki 90, a matsayin martani.

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa tun a watan Mayun da ya gabata, Washington da Beijing sun yi sa-in-sa dangane da harajin da ya kai kashi 145% kan kayayyakin China, da kuma kashi 125% kan kayayyakin Amurka.

Daga bisani, ɓangarorin biyu sun cimma matsaya wacce ta rage harajin da Amurka ta ƙaƙaba wa China zuwa kashi 30%, yayin da na kayayyakin Amurka a China ya ragu zuwa kashi 10%.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *