Gwamnatin sojin Burkina Faso ta rushe dukkanin jam’iyyun siyasa a ƙasar

[ad_1]



Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta sanar da rushe dukkanin jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyin siyasa a ƙasar.

Har ila yau, ta soke dokokin da suka tsara yadda jam’iyyun ke aiki.

An bayyana matakin ne bayan zaman majalisar ministoci da shugaban gwamnatin sojin ƙasar, Kyaftin Ibrahim Traoré, ya jagoranta.

Ministan Harkokin Gudanar da Yankuna da Sufuri, Émile Zerbo, ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin sauya tsarin tafiyar da mulkin ƙasar.

A cewar gwamnatin, yawaitar jam’iyyun siyasa na haddasa rarrabuwar kawuna a tsakanin ’yan ƙasar tare da raunana haɗin kai da zaman lafiya.

“Manufar wannan mataki ita ce kare haɗin kan ƙasa, inganta aikin gwamnati, da kuma buɗe hanyar kafa sabon tsarin siyasa,” in ji fadar shugaban ƙasar.

Cikin sabon umarni, duk kadarori da dukiyoyin da ke hannun jam’iyyun siyasar da aka rushe za su koma hannun gwamnati.

Zerbo, ya ƙara da cewa za a tura daftarin dokar tabbatar da wannan mataki zuwa Majalisar Dokokin Riƙo na ƙasar nan ba da jimawa ba domin amincewa.

Kafin sojoji su karɓi mulki, Burkina Faso tana da jam’iyyun siyasa sama da guda 100 da aka yi wa rajista.

Amma jam’iyyu 15 ne kaɗai ke da wakilci a majalisar dokokin ƙasar bayan zaɓen 2020.

Bayan Kyaftin Traoré ya karɓi mulki ta hanyar juyin mulki a watan Satumban 2022, an umarci jam’iyyun siyasa da su dakatar da ayyukansu a matsayin wani ɓangare na tsarin miƙa mulki.

A wannan zama na majalisar ministoci, gwamnati ta kuma amince da sabon shirin bunƙasa ƙasa na shekaru biyar mai suna “Reliance Plan.”

Shirin zai gudana daga 2026 zuwa 2030, kuma an ƙiyasta kuɗinsa da FCFA tiriliyan 36 (kimanin dala biliyan 65).


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *