Manyan sojojin Rasha da aka kashe

[ad_1]



Shugaban Sashen Bayar da Horo da Ayyuka na Rundunar Sojin Rasha, ya mutu a wani harin bom da aka dasa a karkashin motarsa a safiyar Litinin 22 ga watan Disamba, 2025.

Kisan Sarvarov shi ne na baya-bayan nan a jerin jami’an soja da sauran masu goyon bayan yaƙin da Rasha ta kaddamar a Ukraine a watan Fabrairu 2022.

Ga wasu shahararru daga cikinsu:

1- Laftanar-Janar Yaroslav Moskalik:

Mai shekaru 59, ya mutu sakamakon bam da aka dasa a mota a kusa da Moscow a ranar 25 ga watan Afrilu, 2025. Moskalik shi ne mataimakin shugaban Sashen Babban Ayyuka na Rundunar Sojojin Rasha.

2 – Laftanar-Jarar Irorgy Crillov:

Shugaban Rundunar Kare Sojojin Rasha daga Makaman Nukiliya, Sinadarai da Halittu na Rasha, ya mutu tare da direbansa bayan tashin wani bam da aka ɓoye a keke mai amfani da lantarkia a birnin Moscow a 17 Disamba, 2024.

3- Kyaftin Valery Trankovsky:

A ranar 13 ga Nuwamba, 2024, wani bam da aka dasa a ƙarƙashin mota ya kashe wani sojan Rasha a Sevastopol, da ke yankin Crimea da Rasha ta mamaye. Wata majiyar tsaron Ukraine ta  ce Kyaftin Valery Trankovsky, daga rundunar ruwa ta Rasha, shi ne wanda Ukraine take zargi aikata laifukan yaƙi saboda umartar harin makamai masu linzami kan fararen hula.

4- Stanislav Rzhitsky:

An harbe Jami’in sojan Rasha da ya jagoranci jirgin ruwan karkashin teku a Bahar Maliya kuma aka saka sunansa a jerin masu laifin yaƙi na Ukraine, Stanislav Rzhitsky, har lahira a yayin da yake gudu domin motsa jiki da safe a birnin Krasnodar na kudu.

5-Vladlen Tatarsky:

Dan jaridar intanet mai goyon bayan yaƙin Rasha, ya mutu sakamakon harin bam da aka ɓoye cikin wani ƙaramin mutum-mutumi da wata mace ta ba shi a wani gidan shan kofi da ke birnin St Petersburg 2 ga Afrilu, 2023.

6- Darya Dugina:

A  ranar 20 ga Agusta, 2022 ’yar wani shahararren mai ra’ayin kishin ƙasa mai goyon bayan yaƙi, ta mutu sakamakon bam da aka dasa a mota a yankin Moscow.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *