An Kama Mata 2 Bisa Zargin Shigar Da Miyagun Ƙwayoyi Gidan Gyaran Hali Na Kano

[ad_1]

Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa (NCoS) a Jihar Kano ta kama mata biyu bisa zargin ƙoƙarin shigar da miyagun ƙwayoyi gidan gyaran hali da ke Goron Dutse. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar a Kano, Musbahu Lawan Nassarawa, ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta bayyana cewa an cafke matan ne a yayin binciken tsaro na yau da kullum da ake yi a ranar Lahadi, 21 ga Disamba, 2025. Waɗanda ake zargin, Maryam Ali da Hauwa Musa, masu shekaru tsakanin 19 zuwa 20, dukkansu ƴan Jihar Kano ne.

  • Ganduje Ya Dakatar Da Shirin Kafa Hukumar Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano
  • Gobara Ta Haddasa Mummunar Asara A Kasuwar Kayan Katako A Kano

Nassarawa ya ce an kama su ne yayin da suke ƙoƙarin shiga gidan gyaran hali dauke da wasu abubuwa da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne. Binciken farko ya nuna cewa an yi yunƙurin shigar da ƙwayoyin ne domin bai wa wasu fursunoni a cikin gidan, lamarin da hukumar ta bayyana a matsayin babban karya doka da ƙa’idojin NCoS.

Hukumar ta ce an miƙa matan ga Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakin doka. NCoS ta jaddada cewa ba za ta lamunci duk wani nau’in haramtattun ayyuka a gidajen gyaran hali ba, tare da gargaɗin jama’a da su mutunta dokokin ziyara, domin duk wanda ya karya su zai fuskanci hukunci bisa doka.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *