KEDCO ya zargi TCN kan ƙarancin wutar lantarkin da ake samu a Arewa maso Yamma
[ad_1]
Kamfanin rarraba wutar lantarki na shiyyar Kano (KEDCO) ya ce matsalolin da ake ta fama da su wajen samar da wutar lantarki a Kano, Katsina da Jigawa da sauran jihohin Arewa maso Yamma na da alaƙa da matsalolin da suke fuskanta daga gwamnatin tarayya.
Kamfanin ya ya nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta ɗaukar mataki kan matsalolin, yana mai cewa hakan na mayar da jihohin koma-baya wajen samun wutar.
A cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da jama’a na kamfanin, Sani Bala Sani, ya fitar ranar Alhamis, KEDCO ya ce yana dogaro ne kacokam da hanyoyi biyu kawai na dakon wutar daga Kaduna da Jos domin samun wuta zuwa shiyyar Kano.
Kamfanin ya ce wannan ƙarancin hanyoyin ya sa yankin ya zama yana yawan fuskantar katsewar wuta duk lokacin da matsala ta taso a ɗaya daga cikin layukan.
KEDCO ya jaddada bukatar ƙara tsaro, gyare-gyare da faɗaɗa ƙarfin layin dakon wutar a kan hanyar Shiroro–Mando–Kano.
Ta kuma nuna cewa katsewar wuta da ake yawan samu a ƙarshen mako sakamakon gyare-gyare, ciki har da shigar da wayar lantarki ta ƙarƙashin ƙasa (OPGW), na janyo cikas ga masana’antu da rayuwar al’umma.
Kamfanin ya roƙi gwamnatin tarayya, ta hannun ma’aikatar wuta, da ta umarci Kamfanin Dakon Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN) da ta fifita manyan ayyukan dakon wutar tare da hanzarta gyare-gyaren da ake yi.
Ya ce daidaita harkar dakon wutar na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasar tattalin arziki da kuma samar da wutar lantarki mai inganci ga gidaje da kasuwanci.
Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da jama’a ke ta korafi kan yawan katsewar wuta a jihohin Arewa, wanda ya ƙara ta’azzara sakamakon yawan lalacewar layukan dakon wutar da ƙarancin wuta daga babban layin lantarki na ƙasa, musamman yayin da ake tunkarar lokacin zafi.
Binciken Aminiya ya nuna cewa kamfanonin rarraba wuta na Arewa sun fi samun ƙarancin rabon wuta daga babban layin lantarki na ƙasa a ’yan watannin nan idan aka kwatanta da na Kudancin ƙasar, saboda yawan lalacewar kayayyakin dakon da kuma yawan gyare-gyaren da ake musu.
Ko a farkon bara, yawancin jihohin Arewa sun shafe kusan makonni biyu ba tare da wuta ba bayan da aka ce ’yan bindiga sun kai hari kan layukan dakon wutar a lokacin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link