Bunkasar Tattalin Arzikin Sin Zai Samar Da Tabbaci Ga Duniya Mai Fuskantar Sauyin Yanayi

[ad_1]

A yau Juma’a 6 ga wannan wata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana cewa, a yayin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14, kasar Sin ta samu babban ci gaban tattalin arziki, inda yawan karuwar tattalin arzikin kasar na shekaru 5 ya zarce Yuan trilian 35. An samu wannan kyakkyawan sakamako ne yayin da Sin take fuskantar kalubale daga kasashen waje, da kuma wasu matsaloli a cikin gida, wanda hakan ya shaida cewa, Sin tana da karfin raya tattalin arzikinta.

Mao Ning ta yi nuni da cewa, kasar Sin za ta bi sabon tunanin raya kasa, da kafa sabon tsarin raya kasa, da sa kaimi ga samun ci gaba mai inganci, da inganta tattalin arziki yadda ya kamata. Kana za a kara bude kofa ga kasashen waje, da kiyaye yin hadin gwiwa da samun moriyar juna, don sa fasahohin Sin na samun ci gaba su amfani jama’ar kasa da kasa baki daya, yayin da kuma bunkasar tattalin arzikin kasar zai samar da tabbaci ga duniya mai fuskar sauyin yanayi.

Ban da wannan kuma, game da batun kasar Iran, Mao Ning ta bayyana cewa, Sin na adawa da matakin kasashen Amurka da Isra’ila, na sabawa dokokin kasa da kasa, da kai harin soja kan kasar Iran, kana Sin tana goyon bayan Iran, wajen tabbatar da ikon mulkin kai, da mulkin cikakkun yankunan kasar, da kare mutuncin al’ummar kasar da kuma moriyarta. Har ila yau, kasar Sin tana kira da a daidaita rikicin da ya barke ta hanyar siyasa da diplomasiyya, tana kuma kira da a dakatar da daukar matakan soja, da hana yaduwar yaki, da hana tsanantar yanayin da ake ciki baki daya. (Zainab Zhang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *