Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Tsohon Shugaban NNPC Kan Ɓatan Naira Tiriliyan 210
[ad_1]
Kwamitin Asusun Jama’a na Majalisar Dattawa, ya gayyaci tsohon Shugaban Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari, domin ya yi bayani kan zargin ɓatan naira tiriliyan 210 da bai yi cikakken bayani a kansu ba tsakanin shekarar 2017 zuwa 2023.
Haka kuma an gayyaci tsohon Babban Jami’in Kuɗi na kamfanin, Umar Ajia Isa, da tsohon Babban Manajan National Petroleum Investment Management Services (NAPIMS), Bala Wunti.
- Yadda Manyan Taruka Biyu Na Sin Ke Zamowa Madubin Turbar Ci Gaban Kasar
- ISWAP Sun Hallaka Sojoji 14 A Borno
Shugaban kwamitin, Aliyu Wadada, ya ce sun yanke wannan hukunci ne bayan duba rahotannin binciken kuɗi na kamfanin.
Ya kuma yi gargaɗin cewa za su iya bayar da sammacin kame idan waɗanda aka gayyata suka kasa halarta a lokacin da aka buƙace su.
A cewarsa, rahotannin binciken sun nuna cewa akwai naira tiriliyan 103 da naira tiriliyan 107 da ba a yi cikakken bayani a kansu ba, wanda jimillarsu ta kai naira tiriliyan 210.
Ya ce NNPCL ta bayyana cewa tiriliyan 103 kuɗin da abokan hulɗar kamfanin a harkar haɗin gwiwar mai suka kashe ne tsakanin 2017 da 2023, amma kwamitin ya ce wannan bayani bai gamsar da shi ba.
Haka kuma kamfanin ya rubuta naira tiriliyan 107 a matsayin kuɗaɗen tallafin mai da sauran basussuka a cikin rahoton kuɗinsa na shekarar 2023.
Kwamitin ya kuma yi tambaya kan naira biliyan biyar da aka ce an kashe wajen sauya sunan kamfanin daga Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) zuwa NNPCL.
Hakazalika, an umarci ofishin babban mai bincike da ta gudanar da cikakken binciken kuɗi kan asusun kamfanin a wannan lokaci.
Kwamitin ya ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen tafiyar da kuɗaɗen gwamnati.
[ad_2]
Source link