Zan kasance cikin masu zaɓen sabon jagoran addinin Iran —Trump
[ad_1]
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ya kamata ya kasance yana cikin waɗanda za su zaɓi sabon shugaban jagoran addinin Iran.
Trump ya bayyana haka ne a zantawarsa da kafar yaxa labarai ta Axios, inda ya ce yana kyautata zaton jamhuriyar Musuluncin ta Iran za ta zaɓi ɗan marigayi Ayataullah Khamna’i, wato Mojtaba Ali Khamna’i a matsayin sabon jagora, amma Trump ya ce lamari ne da ba zai taɓa amincewa da shi ba.
“Lokacinsu kawai suke ɓatawa. Ɗan Khamenei ba shi da nauyin da zai kai matsayin. Dole ne in shiga tsakani wajen naɗin, kamar yadda aka yi da Delcy a Venezuela,” Cewar Trump
Shugaban na Amurka yana nufin Delcy Rodríguez, wadda ta karɓi ragamar mulki a Venezuela bayan dakarun Amurka sun kamo tsohon shugaban ƙasar, Nicolás Maduro, a farkon wannan shekarar.
Haka kuma, Trump ya bayyana cewa zai yi watsi da kowane magaji da zai ci gaba da manufofin marigayi shugaban Iran.
“Ɗan Khamenei ba karɓaɓbe ba ne a gare ni. Muna son wanda zai kawo daidaito da zaman lafiya a Iran,” in ji shi.
Ya yi gargaɗin cewa naɗa shugaban da zai bi sawun tsohon babban jagoran na iya tilasta wa Amurka sake shiga yaƙi da Iran “nan da shekaru biyar.”
Har yanzu cibiyar ƙwararru, wadda ita ce ke da alhakin naɗa sabon jagoran, ba ta sanar da wanda zai gaji Ayatollah Ali Khamna’i ba, wanda harin Amurka da Isra’ila ya kashe a birnin Tehran.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link