Fiye da mutum 300,000 sun yi hijira saboda matsalar tsaro a Neja
[ad_1]
Gwamnan Jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya bayyana cewa fiye da mutane 300,000 ne suka tsere daga gidajensu a fadin ƙananan hukumomi sama da 10 sakamakon hare-haren ’yan bindiga a jihar.
Gwamna Bago ya bayyana hakan ne yayin da yake hira da manema labarai a Minna bayan karɓar tallafin jin-ƙai daga gwamnatin tarayya, inda ya ce girman matsalar ya fi yadda mutane da dama ke zato.
Ya bayyana cewa a halin yanzu abin da gwamnati ke da shi ƙididdiga ce kawai, “saboda a halin yanzu ba mu da haƙiƙanin adadin saboda hare-haren na ci gaba da faruwa. Amma a ƙiyasin da muka yi, muna da sama da mutane 300,000 da suka rasa muhallansu a fiye da ƙananan hukumomi 10,” in ji gwamnan.
Ya ce tantance adadin mutanen da aka sace, ko aka kashe ko aka tilasta musu yin hijira ba abu ne mai sauƙi ba, duba da yanayin tsaro da kuma faɗin dazukan da ’yan bindiga ke amfani da su wajen ɓoyewa da kai hare-hare kan ƙauyuka.
Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa na aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro da gwamnatin tarayya domin dawo da zaman lafiya, tare da ba jami’an tsaro cikakken goyon baya ta fuskar kayan aiki, motoci da sauran buƙatu.
Ya bayyana fatan cewa matakan tsaro da ake aiwatarwa a yanzu za su ba wa mutanen da suka yi hijira damar komawa gidajensu cikin aminci da kuma ci gaba da rayuwarsu ta yau da kullum, musamman noma da kasuwanci da hare-haren suka durƙusar da su.
Jihar Neja na daga cikin jihohin Arewa da suka fi fuskantar matsalar ’yan bindiga, lamarin da ya haddasa asarar rayuka, sace-sace da tarwatsa al’ummomi da dama, musamman a yankunan karkara.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link