‘Yansanda Sun Damke ‘Yan Fashi 10 Gami Da Kwato Naira Miliyan 100

[ad_1]

Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Oyo ta kama mutum 10 da ake zargi da fashi da makami, tare da kwato kayayyaki da darajarsu ta kai kusan Naira miliyan 100 a yankin Genesis Hotel da ke Challenge, Ibadan.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Olayinka Ayanlade ya fitar a ranar Lahadi a Ibadan, ya bayyana sunayen wadanda ake zargin kamar haka: Mukaila Omorayo mai shekara 48, Adekanbi Adesola mai shekara 39, Ahmed Oderinlo mai shekara 38, Samuel Omoseyin mai shekara 53, Ramon Saheed mai shekara 52, Monilola Ajayi mai shekara 58, Akanbi Bisi mai shekara 51, Wasilat Abdullahi mai shekara 48, Bolaji Tanimola mai shekara 51, da Adeola Oyesina mai shekara 51.

  • Tallafin Abinci Na Gaggawa Daga Sin Ya Isa Togo
  • 2027: ADC Na Duba Yiwuwar Fitar Da Dan Takarar Shugaban Kasa Ta Hanyar Yarjejeniya — Kakakin Jam’iyya

Ya ce an kwato kayayyaki masu yawa daga hannunsu, ciki har da: Na’urorin sanyaya iska guda 40. Injin wanki 10. Motar babur din lantarki 1. Kayan shafawa iri-iri. Injin yankan 7. Kwalaye 15 na fitilun LED. Kwalaye 25 na manne (furniture gum) Kayan sassan manyan motoci (trailer 0spare parts) Kayan gyaran gashi, wig, chin chin. Da kayan daki da na fenti

Kakakin ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun yi sintiri na makonni bayan samun sahihin bayanan sirri kafin su kai farmaki tare da cafke wannan kungiya a maboyarsu da ke cikin yankin Genesis Hotel.

Ya kara da cewa kungiyar na aikata laifukan fashi da makami tare da satar kwantena da kayan da ake jigilar su, sannan suna aiki a jihohi daban-daban. An kama su ne a wurin da suke boye, tare da kwato kayayyakin da suka sata.

Ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifukansu kuma suna taimaka wa bincike, wanda ke taimakawa wajen gano sauran mambobin kungiyar da ke gudu.

Kwamishinan ‘yansanda na jihar, Olugbenga Abimbola, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin bisa kwarewa da jajircewa. Ya kuma gode wa jama’a bisa bayar da sahihan bayanan sirri da ke taimakawa wajen yaki da laifuka.

Rundunar ta kuma yi kira ga masu otal-otal da su ba da hadin kai ga ‘yansanda, inda ta gargadi cewa wasu masu laifi kan fake a otal-otal domin shirya aikata miyagun ayyuka. An kuma gayyaci masu kula da otal din da lamarin ya shafa domin bincike.

Rundunar ta jaddada aniyarta ta kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da kira ga al’umma da su kasance masu lura da kuma kai rahoton duk wani abin da ke da alamar tuhuma ga hukumomin tsaro mafi kusa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *