Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta Nuna Yanzu Duniya Ta Fi Mutunta Sin Fiye Da Amurka
[ad_1]
Wani bincike da kamfanin Gallup ya gudanar ya gano cewa, a shekarar 2025, Sin ta sha gaban Amurka wajen kimanta samun amincewar duniya, inda matsakaicin kashi 36 cikin 100 na mutanen da suka kada kuri’ar jin ra’ayoyi suka amince da jagorancin Sin, idan aka kwatanta da kashi 31 cikin 100 da Amurka ta samu.
Rahoton Gallup da aka fitar jiya Jumma’a ya ce tazarar kashi biyar da Sin ta samu a kan Amurka ita ce mafi girma da Sin ta taba samu a cikin kusan shekaru 20 da suka gabata.
A cewar rahoton, sauyin da aka samu a baya-bayan nan ya nuna raguwar darajar Amurka yayin da kuma ta kasar Sin ta karu. Matsakaicin kason amincewa da jagorancin Amurka ya ragu daga kashi 39 cikin 100 a shekarar 2024 zuwa kashi 31 cikin 100 a shekarar 2025, inda ya koma mataki na kasa da ya taba kasancewa a baya, yayin da kason amincewa da Sin kuma ya karu daga kashi 32 cikin 100 zuwa 36 cikin 100.
An samu sabbin sakamakon ne daga binciken Gallup da aka gudanar a shekarar 2025 a kasashe fiye da 130, inda aka samu shigar masu amsa tambayoyi kusan 1,000 a kowace kasa. Bugu da kari, binciken bai ma hada da sabbin matakan manufofin ketare na Amurka daga farkon shekarar 2026 ba, wanda a ciki har da harin da ta kaddamar kan kasar Iran da kuma janyewarta daga kungiyoyi 66 na kasa da kasa. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link