Gobara: An yi asarar kayan N800m a Kano — Hukuma
[ad_1]
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta bayyana an yi asarar dukiyar kusan Naira miliyan 800, sakamakon gobara da ta tashi a kasuwar Kwalema da ke unguwar Dakata a Ƙaramar Hukumar Nassarawa.
Gobarar ta tashi ne a wani kamfani da ake kira Fatima Crossion and Recycling da ke yankin.
Mai magana da yawun hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce sashen agajin gaggawa ya samu kiran waya daga wani mutum mai suna Joseph wanda ya sanar da su tashin gobarar.
Jami’an kashe gobara daga hedikwatar hukumar da na yankin Dakata da Rijiyar Zaki ne sun garzaya wajen.
Da isarsu, suka tarar da gini mai girman kusan ƙafa 300 da 200 yana ci da wuta.
Ginin ya kasu kashi huɗu (A, B, C da D), sannan yana da kusan rumfuna 506, inda kusan rumfuna 100 suka ƙone ƙurmus.
Hukumar ta ce ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon wutar da wasu yara suka kunna domin ɗumama jikinsu saboda yanayin sanyi da ake ciki.
An shawo kan gobarar ne ta hanyar haɗin gwiwar jami’an kashe gobara da suka yi amfani da motoci huɗu, wanda ya hana wutar yaɗuwa zuwa sauran sassan ginin.
Daraktan hukumar ya shawarci jama’a da su riƙa ɗaukar matakan kariya, musamman guje wa amfani da wuta a wuraren jama’a da masana’antu suke domin kaucewa irin wannan a nan gaba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link