Darussa Daga Ramadan Na (2)
[ad_1]
A cikin watan Ramalana, ba muna koyon yadda za mu hana kanmu ci da sha ba.kawai, a’a, muna koyon yadda za mu daraja lokaci da sarrafa shi cikin tsari mai kyau. Addinin Musulunci ya gina rayuwar mumini a bisa ladabi da kiyaye iyakoki, musamman iyakar lokaci. Allah Maɗaukaki Ya faɗa mana a cikin Al-ƙur’ani, cikin Suratul Baƙarati aya ta 187 cewa: “Kuma ku ci ku sha har sai farin zare ya bayyana a gare ku daga baƙin zare na alfijir, sa’an nan kuma ku cika azumi zuwa dare”
Wannan aya tana koyar da mu cewa mintuna kaɗan na iya sauya hukunci. Shan ɗigon ruwa guda bayan ketowar alfijir na iya karya azumi, alhali kuwa minti ɗaya kafin haka halal ne. Wannan yana nuna mana cewa lokaci a Musulunci ba abu ne na wasa ba, sai dai ma’auni ne da ake auna biyayya da saɓa wa Allah.
- SAHUR (Falalarsa Da Fa’idojinsa) Na 4
- SAHUR (Falalarsa Da Fa’idojinsa) Na 5
Daga nan ne mumini yake fahimtar cewa:
Rayuwa tana tafiya ne bisa ƙa’ida da tsari.
Ƙananan abubuwa kan iya haifar da manyan sakamako. Kula da lokaci alama ce ta tsoron Allah (taƙawa).
Azumi yana koya mana kulawa da agogo, lura da alfijir da faduwar rana, da kuma kiyaye iyakar da Allah Ya shimfiɗa. Idan mumini ya iya tsare kansa daga ruwa da abinci saboda tsoron Allah, to ya fi dacewa ya iya tsare harshensa daga ƙarya, da zuciyarsa daga hassada, da aikinsa daga zalunci, da kuma riya. Saboda haka, Ramalana makaranta ce ta horo:
1. Makarantar tsoron Allah.
2. Makarantar tsari ne.
3. Kuma makarantar darajta lokaci.
Idan muka fahimci wannan darasi, za mu gane cewa ba yunwa da ƙishirwa ne manufar azumi ba, sai dai gina mutum mai ladabi da sanin darajar kowane daƙiƙa a rayuwarsa. Wannan shi ne ilimin da Ramalana ke koyarwa, kuma wannan shi ne hikimar da ke ɓoye a bayan kiyaye minti guda na alfijir.
Abu Razina Nuhu Ubale Ibrahim Paki
[ad_2]
Source link