An sanya tukwicin N10m domin kama makasan limamin coci a Enugu
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Enugu ta tanadi tukwuicin naira miliyan goma ga duk mutumin da ya taimaka aka kama waɗanda ake zargi da kashe fitaccen limamin cocin Katolika, Matthew Eya.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa tabbatar da alƙawari da Kwamishinan Labarai, Malachy Agbo, ya fitar ranar a Asabar.
Wasu ‘yan bindiga ne suka harbe Mr Eya, limamin cocin katolika ta Saint Charles Catholic Church da ke garin Eha-Ndiagu ranar Juma’a a kan hanyar Eha-Alumonah–Eha-Ndiagu da ke ƙaramar hukumar Nsukka.
Rahotanni sun ce ’yan bindiga sun yi wa limamin kwanton-ɓauna wanda suke harbe a yayin da yake kan hanyar komawa gida daga yankin Enugu Urban.
Limamin cocin mamba ne a Cocin Nsukka Catholic Diocese, wadda ta tabbatar da kisan nasa.
A sanarwar da Mista Agbo ya fitar, ya ambato gwamnatin Enugu tana “yin Allah wadai da kakkausar muryar” bisa “mummunan kisan” da aka yi wa limanin cocin.
“Gwamnatin Enugu tana miƙa saƙon ta’aziyyarta ga iyalan limanin cocin, da Catholic Diocese ta Nsukka, da kuma mabiya ɗarikar Katolika baki ɗaya bisa wannan iftila’i,” a cewar kwamishinan.
Ya bayyana makasan a matsayin “matsorata” waɗanda suka aiwatar da kisan “rashin imani”, inda ya sha alwashin cewa gwamnati za ta kama ‘yan bindigar da suka yi wannan aika-aika.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link