An tsinci gawar saurayi a gefen kudiddifi a Kalaba
[ad_1]
An tsinci gawar wani saurayi mai suna Daniel Ekanen, mai kimanin shekaru 18, a gefen wani kudiddifi da ke unguwar Ikot Effanga a Ƙaramar Hukumar Kalaba, Jihar Kuros Riba.
Lamarin ya jefa firgici a zukata da kuma zaman dar-dar a cikin mazauna yankin, inda aka ruwaito cewa an kawo marigayin ne wurin dangin mahaifinsa daga ƙauyen Ikot Offiong da ke ƙaramar hukumar Odukpani a jihar.
Rahotanni sun nuna cewa ana zargin masu tsafi da sassan jikin ɗan adam ne suka yi kisan, domin kuwa an yanke kansa kafin a jefar da gawarsa a gefen kudiddifin.
Wani daga cikin ’yan uwan marigayin ya shaida wa Aminiya cewa saurayin ya fita ne domin ɗebo kayan miya a gona, amma daga nan aka rasa shi, sai daga baya aka tsinci gawarsa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamishinan ’yan sanda na Jihar Kuros Riba, Rashid Afegbua, ya ce sun tura jami’an tsaro daga rundunar Dragon Squad da kuma ofishin ’yan sanda na yankin Ikot Omin domin gudanar da bincike kan wannan mummunan lamari.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link