Sarkin Musulmi ya ayyana Litinin 1 ga watan Rabi’ul Awwal
[ad_1]
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya tabbatar da cewa gobe Litinin, 25 ga watan Agusta, 2025, ita ce za ta zama 1 ga watan Rabi’ul Awwal, 1447 bayan hijira.
Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin shugaban kwamitin kula da harkokin addini a majalisar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda ya bayyana cewa ba a samu labarin ganin sabon wata na Rabi’ul Awwal a ranar Asabar, 29 ga Safar ba.
Farfesa Sambo wanda kuma shi ne Wazirin Sakkwato, ya ce saboda haka, Lahadi, 24 ga watan Agustan 2025, za ta zama 30 ga watan Safar, sannan kuma bisa ga tsarin Musulunci, Sarkin Musulmi ya ayyana Litinin a matsayin farkon watan Rabi’ul Auwal.
“Bisa ga rahotannin da muka karɓa daga kwamitin ganin wata da na harkokin addini na kasa, babu wanda ya tabbatar da ganin jinjirin watan Rabi’ul Awwal a ranar Asabar, don haka Sarkin Musulmi ya amince cewa Litinin ce farkon watan,” in ji shi.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link