Ci Gaban Sin Ya Ba Da Kwarin Gwiwa Ga Duniya A Shekarar 2026

[ad_1]

A jajibirin sabuwar shekara, shugaban Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi na taya murnar sabuwar shekara ta 2026. Kafafen watsa labarai na duniya sun mayar da hankali kan jawabin, wanda ya nuna kwarin gwiwa da karfin da Sin ke da su.

Wannan kwarin gwiwa, ya samo asali ne daga karfin ci gaban kasar Sin mai inganci. A shekarar da ta gabata, an kiyasta cewa jimillar kudaden tattalin arziki na kasar Sin ta kai yuan tiriliyan 140, wanda ke ci gaba da bayar da gudummawar kusan kashi 30% ga ci gaban tattalin arzikin duniya, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga ci gaban duniya yayin da ya fuskanci kalubale.

Wannan kwarin gwiwa, ya kuma fito ne daga hikimar Sin da gudummawarta wajen inganta zaman lafiya da kyautata tsarin shugabanci a duniya. A shekarar da ta gabata, a matsayinta na babbar kasa da nauyi ya rataya a wuyanta, kasar Sin ta ci gaba da bunkasa tattaunawar zaman lafiya don rage rikice-rikicen duniya. A taron kolin Tianjin na kungiyar SCO, shugaba Xi ya gabatar da shawarar inganta jagorancin duniya, wanda ya sami goyon baya daga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 150.

Wannan kwarin gwiwa, ya kuma fito ne daga nauyin da Sin ta dauka na dakile ra’ayin bangaranci da kafa shinge ta hanyar bude kofa da hadin gwiwa. Ganin yadda Sin ke fuskantar ra’ayin bangaranci da kafa shinge, ta yi kira da a “hada hannu” maimakon “ware hannu”, ta kuma ci gaba da inganta bude kofa ga kasashen waje ta hanyar hadin gwiwa.

A shekarar 2026, kasar Sin mai kwarin gwiwa, bude kofa, da kuma hangen nesa za ta kara ba da kwarin gwiwa da karfi ga duniya.(Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *