Jami’ar Jos ta dage jarrabawa saboda tashin hankali

[ad_1]



Hukumar Gudanarwar Jami’ar Jos ta sanar da dage dukkan jarrabawar da aka shirya gudanarwa a ranar Litinin, sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan harin ’yan bindiga a unguwar Anguwan Rukuba da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato.

A sanarwar da Mataimakin Rajistara na Sashen Bayanai da Hulɗa da Jama’a, Emmanuel Madugu, ya fitar a ranar Lahadi, jami’ar ta ce lamarin ya jawo fargaba a cikin al’ummar da ke kewaye da jami’ar, inda ma’aikata da ɗalibai da dama ke zaune.

Ganau sun bayyana cewa maharan da ke kan babura sun kutsa cikin unguwar da misalin ƙarfe 7:30 na dare, suna harbi barkatai, lamarin da ya jawo firgici da asarar rayuka.

An kashe mutane da dama, wasu kuma sun jikkata, lamarin da ya fusata matasa suka toshe hanya, suna kai wa direbobin baburan haya da fasinjoji hare-hare.

Sanarwar jami’ar ta ce, duk jarrabawar da aka shirya a ranar Litinin 30 da Talata 31 ga Maris, 2026, an dage su, za a kuma sake tsara jadawalin.

Ta kuma shawarci ɗalibai da ma’aikata su kasance cikin shiri da kulawa sosai da motsinsu, a cikin da wajen jami’a.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa kada a fita da sassafe, kuma duk wani alamar barazana ga zaman lafiya a gaggauta sanar da jami’an tsaro na jami’ar a lambar 08035895323.

Hukumar gudanarwar jami’ar ta ce tana ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro don tabbatar da tsaron rayukan al’ummar jami’ar, tare da alkawarin ci gaba da sanar da ƙarin bayani a nan gaba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *