Arsenal Na Tattaunawa Da Declan Rice Kan Tsawaita Kwantiraginsa A Ƙungiyar
[ad_1]
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta fara tattaunawa da ɗan wasanta, Declan Rice, kan yiwuwar sanya hannu kan sabon kwantiragi a ƙungiyar.
Kwantiragin Rice na yanzu zai ƙare cikin shekaru biyu, amma tun da farko akwai zaɓin tsawaita wa’adin da ƙarin watanni 12.
- Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Na Kokarin Cika Wa’adin Dokar Zabe
- Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 24
Arsenal, wadda ke jan ragamar teburin gasar Premier League, na fatan ɗan wasan na tawagar Ingila ya sadaukar da shekaru masu yawa ga ƙungiyar.
Sabon tayin zai haɗa da ƙarin albashi domin zama a matsayin ɗaya daga cikin ‘yan wasan da suka fi samun albashi mai tsoka a Arsenal.
Kwanan nan, Bukayo Saka ya sanya hannu kan sabon kwantiragi na shekaru huɗu da rabi wanda zai sa ya karɓi aƙalla £300,000 a kowane mako.
Ana hasashen kwantiragin Rice zai kai kimanin £240,000 a kowane mako, kuma tattaunawar da aka fara an bayyana ta a matsayin mataki na farko wajen ganin Declan ya amince da sabon kwantiragi.
Tun bayan da ya koma Arsenal daga West Ham a yarjejeniyar da ta kai £105 miliyan a shekarar 2023, ɗan wasan mai shekaru 27 ya yi suna a matsayin ɗaya daga cikin ‘yan wasa masu kyau a Turai.
Ya riga ya buga wasanni 102 a gasar Premier League da Arsenal.
[ad_2]
Source link