’Yan ta’adda sun banka wa ofishin ’yan sanda wuta, sun sace mutum 6 a Neja
[ad_1]
Wasu gungun ’yan ta’adda sun banka wa ofishin ’yan sanda wuta da ke garin Agwara, a hedikwatar Ƙaramar Hukumar Agwara da ke Jihar Nijar.
Harin wanda ya auku da asubahin ranar Lahadin ya rutsa da wasu mutum akalla shida da aka yi garkuwa da su.
Majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa maharan sun isa yankin da misalin ƙarfe 4:00 na asuba, inda suka yi artabu da jami’an ’yan sanda da manyan makamai, lamarin da ya tilasta wa jami’an tserewa.
Wani mazaunin garin Agwara, Malam Hussaini Mohammed, ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho cewa harin ya jefa fargaba a garin, inda mutane da dama suka tsere domin tsira da rayukansu.
Ya ƙara da cewa an kuma ƙone sashen wani coci da ke yankin.
A cewarsa, bayan ƙona ofishin ’yan sanda ne ’yan ta’addan suka nufi Cocin UMC (United Methodist Church), inda suka yi garkuwa da mutane akalla shida.
Haka kuma, an ruwaito cewa bayan barin Agwara, maharan sun kai hari a al’ummar Sokonbara, inda suka kashe wata mata tare da kwashe kayan abinci.
Majiyoyi sun ce daga cikin waɗanda aka sace akwai tsohon Shugaban Ƙungiyar Malaman Makaranta ta Ƙasa (NUT) na Ƙaramar Hukumar Agwara, Malam Ahmed Burade, tare da matarsa da ’ya’yansa huɗu.
Sai dai bayanai sun ce Malam Ahmed Burade ya tsere ne a yayin musayar wuta tsakanin ’yan ta’addan da ’yan sa-kai, amma matarsa wadda ke jinya da ’ya’yansu huɗu an tafi da su.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Nijar, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar harin, sai dai ya ce ba a samu asarar rai ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link