PDP Ta Yi Allah-wadai Da Sace Ɗalibai Mata A Kebbi



Jam’iyyar PDP ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa wata makaranta ‘yan mata a Jihar Kebbi.

A yayin kai harin, maharan sun kashe mataimakin shugaban makarantar, tare da  sace ɗalibai 25.

PDP ta ce wannan lamari mai ban tausayi yana nuna yadda rashin tsaro ya ƙara ƙamari a Nijeriya.

Jam’iyyar ta zargi gwamnati, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, da rashin kare jama’a.

Jam’iyyar ta bayyana cewa idan gwamnati ta gaza kare jama’arta, to dole ne ta ɗauki alhakin kuma ta magance matsalar, ba ta yi watsi da ita ba.

PDP ta jajanta wa iyayen ɗaliban da aka sace da kuma iyalan mataimakin shugaban makarantar da aka kashe.

Ta kuma aike saƙon ta’aziyyarta ga makarantar da gwamnatin Jihar Kebbi.

Jam’iyyar ta nuna damuwa kan yadda sace-sacen mutane a jihohi kamar Nasarawa, Filato, Kano, da Katsina suka yawaita a baya-bayan nan.

Saboda haka, PDP ta yi kira ga shugaba Tinubu da ya san yadda zai kare rayuka da dukiyoyim al’ummar Njeriya domin a kawo ƙarshen matsalar.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *