Tattalin Arzikin Nijeriya Ya Bunkasa A 2025 — Minista

[ad_1]

Gwamnatin tarayya ta ce tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da bunkasa a kowane wata na tsawon watanni 12 a jere a shekarar 2025, abin da ke nuna ci gaba mai dorewa a harkokin tattalin arziki duk da kalubale na duniya da na cikin gida.

Ministan Harkokin Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana wannan a ranar Litinin a Abuja yayin gabatar da rahoton gwamnatinsa na karshen shekara.

  • Mutane 5 Sun Rasu, 35 Sun Jikkata A Harin Bam A Masallaci A Borno
  • Mutane 5 Sun Rasu, 35 Sun Jikkata A Harin Bam A Masallaci A Borno

Idris ya ce wannan ci gaba mai dorewa ya bayyana a cikin (PMI), wani muhimmin ma’auni na amincewar ‘yan kasuwa, wanda ya nuna ci gaba ba tare da katsewa ba a duk shekara.

“Bayanan PMI na baya-bayan nan wanda shi ne muhimmin ma’auni na yanayin kasuwanci sun nuna cewa Nijeriya ta samu watanni 12 a jere cikin bunkasar harkokin tattalin arziki,” in ji shi.

Idris ya bayyana cewa wannan nasara ta nuna karfin sashen tattalin arzikin da ba na mai ba, ko da yake akwai matsin lamba daga hauhawar farashi da rashin tabbas na tattalin arzikin duniya.

A cewar ministan, Jimillar Kadarorin Cikin Gida (GDP) na Nijeriya ya karu da kashi 3.98 cikin dari a kwata na uku na shekarar 2025, inda babban abin da ya ja wannan ci gaba shi ne bunkasar ayyuka, kasuwanci da masana’antu.

Ya kuma ce hauhawar farashin kayayyaki ya ragu na tsawon watanni takwas a jere zuwa kashi 14.45 cikin dari a watan Nuwamba 2025, yayin da ajiyar kudin kasa na waje ya karu zuwa kusan Dala biliyan 44.56.

“Ajiyar kudin kasarmu na waje ya karu zuwa kusan Dala biliyan 44.56, wanda ke samar da kariya mai karfi wacce ke daidaita darajar kudinmu kuma ke ba masu zuba jari na kasa da kasa kwarin gwiwa,” in ji shi.

Idris ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ta dage wajen karfafa daidaiton tattalin arziki na kasa baki daya da tabbatar da cewa alamomin ci gaban tattalin arziki su canza zuwa ingantattun rayuwar ‘yan Nijeriya.

Ya kara da cewa kasafin kudin shekarar 2026 zai bai wa tsaro fifiko, ci gaban ababen more rayuwa, karfafa matasa da jin dadin al’umma domin ci gaba da bunkasa tattalin arzikin da ake samu a yanzu.

“Manufar shekarar 2026 ita ce gina tubalin Nijeriya mai tsaro, mai fafatawa da kuma mai wadata,” in ji ministan, yana mai cewa sauye-sauyen da gwamnatin ta aiwatar suna fara haifar da fa’idodi na dogon lokaci.

Ya bayyana hangen nesa na Shugaba Bola Tinubu ga kasa a matsayin mai jarumta da mai mai da hankali, inda ya tabbatar cewa Nijeriya “Da gaske na kan tafiya” zuwa ci gaba mai dorewa da hadin gwiwa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *